1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhi: Gazawar manzancin Larabawa a Siriya

January 19, 2012

Ana ci gaba da sukan lamirin ƙungiyar haɗin kan Larabawa dangane da tawagar 'yan kallon da ta tura zuwa Siriya, wadda kuma ga alamu ba ta cimma burinta ba. Daniel Scheschkewitz ya rubuta sharhi:

Demonstrators protest against Syria's President Bashar al-Assad in Zabadani, near Damascus Januray 13, 2012. The banner reads, "Go, want to back to my school". REUTERS/Handout (SYRIA - Tags: POLITICS CIVIL UNREST) FOR EDITORIAL USE ONLY. NOT FOR SALE FOR MARKETING OR ADVERTISING CAMPAIGNS. THIS IMAGE HAS BEEN SUPPLIED BY A THIRD PARTY. IT IS DISTRIBUTED, EXACTLY AS RECEIVED BY REUTERS, AS A SERVICE TO CLIENTS
Masu zanga-zangar adawa da gwamnati a DamascussHoto: Reuters

Babu wata alamar gamsuwa daga shugaba Bashar Assad a game da manzancin ƙungiyar ƙasashen Larabawa a Siriya. Hakan kuwa ba abin mamaki ba ne, saboda ainihin maƙasudin manzancin yayi daura da maslahar gwamnatinsa. Nauyin da aka ɗora wa tawagar 'yan kallon ta ƙasashen Larabawa dai shi ne ta sa ido wajen ganin an janye sojojin Siriya daga biranen ƙasar an kuma saki fursinonin siyasa daga gidajen kurkuku.

A baya ga haka an ɗora wa tawagar alhakin taimakawa domin kawo ƙarshen tashin hankali tsakanin gwamnatin Siriya da 'yan adawarta. Amma kuma kwalliya ba ta mayar da kuɗin sabulu game da hakan ba. Tun bayan isar tawagar ƙasar Siriya makonni huɗu da suka wuce, gwamnatin ba ta sassauta ɗaukar dukkan matakan da zata iya ba don murƙushe abokan adawarta.

Shugaba Assad na gabatar da jawabinsa a DamascussHoto: picture-alliance/dpa

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙiyasce cewar aƙalla mutane dubu biyar ne tashin-tashinar ta rutsa da su tun bayan farawarta a watan maris na shekarar da ta wuce. Anja Zorob, mai koyarwa a cibiyar nazarin al'amuran yankin gabas ta tsakiya da arewacin Afirka a jami'ar Berlin ta ce akwai wani muhimmin dalili game da gazawar tawagar wajen lafar da ƙurar rikicin. Domin kuwa tun da farkon fari gwamnatin Siriya ba ta ɗauki manzancin da muhimmanci ba. Kuma a ganin shugaba Assad wannan manzancin wata dama ce a gare shi domin samun ƙarin lokaci. Hakan ma dai na daga cikin dalilan da suka sanya 'yan adawa a Siriyar ke ganin tawagar 'yan kallon ba ta cimma biyan buƙata ba. Har yau ana ci gaba da zub da jini a ƙasar a yayinda ita kuma ƙungiyar haɗin kan Larabawa ba ta da ikon taɓuka kome. Wani ma abin dake ɓata wa 'yan adawar rai shi ne yaba wa gwamnatin shugaba Assad da shugaban tawagar janar Muhammed Mustafa Ahmed al-Dabi ya riƙa yi a ƙarshen watan disemban da ya wuce. Naɗin al-Dabi ma dai ya haifar da mummunan suka saboda kasancewarsa na hannun daman shugaba Al-Bashir, da ake zarginsa da laifukan cin zarafin ɗan-Adam a yaƙin Darfur.

Mustafa al-Dabi shugaban tawagar sa ido ta Larabawa a siriyaHoto: picture-alliance/dpa

Shi dai Assad yayi amfani da saɓanin dake akwai tsakanin ƙasashen ƙungiyar haɗin kan Larabawa. Ga alamu dai ba wani abin dake ci masa tuwo a ƙwarya matsawar da al-Dabi ke ci gaba da jagorantar tawagar. Sannan a ɗaya hannun kuma ƙasashe kamarsu Sudan na ba shi wata dama ta sukan lamirin manufofin ƙungiyar baki ɗaya. A taƙaice dai makonni huɗu bayan tura tawagar zuwa Siriya, murna na neman komawa ciki, dangane da manufar da ƙungiyar haɗin kan Larabawa ta sa gaba. Amma Anja Zorob na ganin mai yiwuwa gazawar tawagar ma ita ce mafi alheri, saboda hakan na ma'ana ne cewar gwamnatin Siriya ba ta cika sharuɗan da aka gindaya mata ba kuma Allah ne kaɗai Ya san irin abin da zai biyo baya.

Mawallafi: Daniel Scheschkewitz/Ahmad Tijani Lawal

Edita: Yahouza Sadissou Madobi