1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhi: Gwamnatocin kama-karya na nasara a Siriya

Kersten Knipp GAT
March 20, 2018

Sojojin Turkiyya sun yi nasarar kafa tuta a Afrin na Siriya. Kasashen da ake gudanar da salon mulkin kama-karya ne za su tsara makomar Siriya in ji Kersten Knipp a cikin sharhin da ya rubuta.

Türkische Armee rückt in Afrin ein
Hoto: picture-alliance/AA

Sojojin Turkiyya sun yi nasarar kafa tuta a Afrin na Siriya bayan da suka shafe kwanaki suna gwabza yaki da Kurdawan yankin. Akwai ma alamun cewa Turkiyya ba za ta bar Siriya da sauri ba bayan da ta mamaye yankin. Wannan nasarar ta sa an kara fahimtar cewa kasashen da ake gudanar da salon mulkin kama karya irin su Turkiyya ne za su tsara makomar Siriya da kasashe da ke makwabtaka da ita, in ji Kersten Knipp a cikin sharhin da ya rubuta.

 

Kusan watanni biyu da suka gabata ne Recep Tayyip Erdogan ya tura da jiragensa na yaki zuwa kasar Syria. Tuni ma hakarsa ta cimma ruwa, inda tun ranar Lahadi, tutar Turkiyya ta fara kadawa a ofishin magajin garin Afrin. Koda yake Erdogan ya bayyana cewa kasarsa ba ta zo da niyar mulkin mallaka ba, amma dukkanin alamun mamaya sun fito fili.
Wai shin tsawon wani lokaci ne Turkiyya za ta zauna a Afrin? Masu sharhi na kasashen Larabawa da na Turai na dasa ayar tambaya a kan wannan batu. Yawancin wadanda suke nuna shakku sun bayyana cewar ba farau ba ne tun da Turkiyya ta mamaye Cyprus a shekarar 1974. Kuma har yanzu akwai sojojin Turkiyyar a wannan tsibirin.
Ko ma me ake ciki dai, an san cewar tutar Turkiyya za ta iya shafe tsawon lokaci tana kadawa a Afrin. Dama Erdogan ya nunar da cewa yana so ya fatattaki Kurdawan da ke fafutuka da makamai daga garin Manbij, zuwa nisan kimanin kilomita 100 yamma da garin. Don haka ake ganin cewar Turkiyya za ta kai hare-hare da manyan makamai a wani birni, inda mutane za su shiga mawuyacin hali. Hasali ma, gumurzu da sojojin Turkiyyar suka yi a Afrin na iya zama somin tabi.

Yakin Siriya da ke halaka dubban mutane ya bai wa fadar mulki ta Ankara dama ta musamman ta farautar wadanda take dangantawa da "'yan ta'adda". Tun shekarun da suka gabata ne Turkiyya ke amfani da wannan salon na amfani da kasashe irin Siriya da Iran da Rasha don tabbatar da dankofe abokan hamayya. Erdogan da kansa ya sanar a makon da ya gabata hanyoyin da zai bi wajen ci gaba da mamaya: inda ya ce "Da farko za mu tsaftace Afrin, sannan Manbij da 'yan tawayen yankunan gabashin Euphrates, ya zuwa iyakarmu da Iraki."

Abin mamakin shi ne yadda gwamnati Siriya ta bar Turkiyya ke cin karenta babu babbaka. Damascus ba ta nuna damuwa game da mamaye wani yanki da maƙwabta suka yi ba, kuma babu wani kokarin na kare rayukan mazauna Afrin. Wannan ba irin martani ba ne da ake jira daga gwamnatin da ta shafe shekaru tana gwabza mummunan yaki da 'yan adawarta ba ne. Amma kuma amsa a fakaice da ke nuna irin alkiblar da ake son dora Siriya a kai ne.

Hoto: Reuters/K. Ashawi

Gaskiyar magana a nan shi ne, wata alama ce da ke nuna cewar Ankara da Damascus sun dade da cimma matsaya ta bayan fage. Sannan kowa ya san cewar kasar Siriya ta durkushe, ba za ta iya nuna wa wadanda za su mamayeta 'yar yatsa ba. Kamar dai yadda Rasha da Iran suka yi a baya, Ankara za ta iya karfafa wannan hanya wajen samun biyan bukata. Erdogan ba shi da wata damuwa dangane da cewa sojojinsa na iya fusatar da Amirkawa, wadanda har yanzu suke aiki a Manbij tare da Kurdawa. 

Bayan shekaru bakwai na yaki, a bayyane yake cewa taswirar Siriya da ma kusan ta dukkanin yankin ta kan canzawa. Siriya za ta zama kasar da ake yi wa mulki mallaka, ko kuma take samun kariya daga masu ruwa da tsaki a mulkinta. Imma makwabta kamar Turkiyya da Iran ne, ko kuma manyan kasashen duniya musamman Rasha ne. A cikin wannan yanayi ne Turkiyya ke neman yada angizonta a kasar. Wannan ya nuna cewar masu salon mulkin kama-karya na samu nasara a Siriya da ma yankin Gabas ta Tsakiya. Kuma za su ci gaba da tasiri na dogon lokaci.