Birnin Sochi a karon farko ya karbi bakuncin babban taron koli tsakanin Afirka da Rasha, an tafka muhawara a bangarori da dama da suka shafi tashar nukiliya, kulla dangantakar kasuwanci da ma gyara babbar matsalar Afrika ta wutar lantarki. Daya daga cikin niyar Rasha shi ne shigar da fasahar kera makamashin nukiliya a nahiyar ta Afirka ta hanyar gina tashoshi masu dan karan tsada.
Sannan Rasha na kokarin habbaka dangantakar aiki tsakanin sojojin kasar da na nahiyar Afirka. Abu ne da za a iya yin maraba da shi idan ba zai kara yaki da rikicin da nahiyar ke fuskanta ba. Duk kasar da ta saka hannu a kan karin sayan makamai to kamar ta kira ma kanta ruwan ne ba ta da lema. Duba da yadda nahiyar ke fama da rikici iri-iri.Ta kowane bangare aka duba Afirka ba ta bukatar ire-iren wadannan alakar da zai kara wa mutanen wahala.