1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhi: Isra'ila da Hamas na gwada 'yar kashi a Gaza

November 15, 2012

A yayin da zaɓen Isra'ila ke tafe, mayaƙan Hamas da na Isra'ila suna amfani da ƙarfin makamai domin ɗaukar hankalin magoya bayansu.

Hoto: Reuters

Yanzu haka mayaƙan Palesɗinawa da sojojin Isra'ila suna ci gaba da kai wa junan su hare-hare da makamai, abin da ya sake tayar da tunanin abubuwan da suka faru na yaƙin Gaza shekaru huɗu da suka wuce. Hakan, inji Bettina Marx, da ta rubuta wannan sharhi, ya ƙara tabbatar da bukatar samun sulhun siyasa cikin gaggawa tsakanin Isra'ilan da Palesɗinawa.

Babu wata ƙasa a wannan duniya tamu da za ta kyale a riƙa kai mata hari da rokoki daga makwabta. Wannan dai shi ne dalilin da Isra'ila ta bayar, lokacin da ta ƙaddamar da matakin ta na ramuwar gayya a baya-bayan nan a yankin Gaza. Wannan kuwa dalili ne da babu mai iya musunta shi, domin alhakin farko dake kan ko wace kasa shine tabbatar da kariya ga al'ummarta. Ba kuma zai yiwu ace al'ummar Israila mazauna kudancin kasar a tsawon shekaru 12, suna ci gaba da fama da hare-haren rokoki daga yankin Gaza ba, yadda yara sukan yi kwana da kwanaki suna wuraren kariya na karkashin kasa, ba kuma tare da mazauna yankin sun sami damar tafiyar da rayuwar su ta yau da kullum ba.

To sai dai wannan hali na kunci ba yan Israila kadai ya shafa ba, har suma mazauna yankin na Gaza miliyan daya da dubu 700 sun kasance a cikinsa. Suma suna da yancin rayuwa tare da tsaro, kuma cikin jin daɗi da walwala, abin da a yanzu, mazauna yankin Gaza sai dai su yi mafarkinsa.

Shugaban kungiyar Hamas Khaled MashaalHoto: picture-alliance/dpa

Tun shekara ta 1991, wato tsawon fiye da shekaru 20 mazauna Gaza suke rayuwa kamar a kurkuku, tare da dannin waya da ya kewaye su. A wancan lokaci, kafin ma a cimma yarjejeniyar zaman lafiya ta Oslo, Isra'ila ta fara ɗaukar matakan rage ikon zirga-zirga tsakanin Palesdinawa a yanikin Gaza da yammacin kogin Jordan. A bayan da aka fara shawarwarin neman zaman lafiya a tsakiyar shekaru na casa'in, Israilan ta kakkafa shingayen waya suka kewaye yankin na Gaza, inda tun daga wannan lokci ma'aikata ne kadai suke samun izinin fita daga yankin dake gabar teku domin shiga aiki a Israila.

A 'yan shekarun baya Israila ta kara tsuke yancin mazauna yankin, wato tun bayan da kungiyar Hamas ta sami nasarar zabe a yankin Israila ta toshe shi gaba daya. Ga mafi yawan mazauna Gaza, inda kashi 60 cikin dari matasa ne da basu wuce shekaru 20 da haihuwa ba, hakan yana nufin basu taba fita daga yankin na Gaza ba. An haife su a kurkuku, sun taso a kurkuku, sun girmna a kurkuku, ba tare da an taba basu damar sanin me ke gudana a sauran duniya ba. Wadannan matasa basu da yanci, basu kuma da fatan samun wata makoma mai haske a rayuwarsu. Kwararrun majalisar dinkin duniya ma sun yi imanin cewar nan da shekaru goma masu zuwa, yankin Gaza zai zama m babu mai iya zama a cikinsa.

Sai dai duka wannan hali ne da Israila da sauran duniya suke masa shakulatin bangaro. Batun neman sulhun siyasa a rikicin yankin gabas ta tsakiya tuni ya daina zama a jerin al'amuran da duniya take maida hankali kansa, sai fa idan an zo zabe a Israila ne yankin Gaza yake taka muhimmiyar rawa, kamar dai shekaru hudu da suka wuce, lokacin da Israilan ta rika kaiwa yankin hare-hare yan makonni kalilan kafin zabe, inda Palesdinawa akalla 1400 suka mutu. Ga ministan tsaro Ehud Barak da 'yar ƙaramar jam'iyar sa take gwagwarmayar ci gaba da rayuwa, wannan yaki yana iya zama wata hanya ta sake shiga majalisar dokoki, to sai dai hakan, ko kuma yaƙin da ya tashi yanzu, ba zai sulhunta rikicin Gaza ko na Gabas ta Tsakiya ba.

Pirayim Ministan Israila Benjamin NetanjahuHoto: dapd

Mawallafi: Bettina Marx/Umaru Aliyu
Edita: Mohammad Nasiru Awal