1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhi: Jamus ta gano aiyukan kungiyoyi na yan Nazi

November 15, 2011

Gwamnatin taraiyar ta jamus tayi alkawarin gudanar da bincike mai tsanani a game da aiyukan wata kungiya ta asiri ta masu ra'ayin yan Nazi wadanda ake zargin su da kashe-kashe tun daga shekarun baya

Ministan cikin gidan Jamus Hans Peter FriedrichHoto: picture alliance/dpa

Gwamnatin taraiyar ta jamus tayi alkawarin gudanar da bincike mai tsanani a game da aiyukan wata kungiya ta asiri ta masu raayin yan Nazi wanda ya kamata a gudanar dashi ba tare da rufa-rufa ba, a kuma gudanar shi cikin gaggawa.

Har yanzu dai babu wata shaida , amma akwai alamu masu karfi dake karfafa zaton cewar tsawon shekaru goma sha biyu wata kungiya ta masu ra'ayin rikau ta yan Nazi daga yankin Zwickau a gabashin Jamus ta kashe mutane mafi yawan su baki yan ci rani dake zaune a nan Jamus da kuma kai hare-hare masu tarin yawa a bankuna. Babu kuma wanda ya lura da cewar kisan jama'a da aka yi, da aka sanya masa suna wai kisan gidan sayar da Döner, kisa ne na wadannan yan Nazi.

Hakan ya kai ga tambayar, shin yaya aka yi har Jamus ta tsinci kanta cikin wnanan hali? Shin ina hukumar leken asiri ta kasar wadda aikin ta ne ta gano irin wadannan masu yiwa tsarin mulkin kasar zagon kasa. Ma'aikatar cikin gida tayi bayanin cewar har ya zuwa yan kwanakin baya, babu wasu alamu masu karfi da suka nuna cewar kungiyar ta masu ra'ayin rikau ta yan Nazi ita ce take da laifin wadannan kashe-kashe. Shin an kasa gano aiyukan kungiyar ne saboda hukumomin leken asiri sun fi maida hankalin su ga aiyukan kungiyoyin musulmi masu matsanancin ra'ayi. Shin hukumomin leken asirin sun dauka cewar duk lokacin da suke so suna iya shawo kan matsalar ta yan Nazi ne a kasar, ta hanyar amfani da masu basu rahotanni a boye domin samun bayanai da suke bukata? Duka wadnanan tambayoyi ne da tilas a yi bincike kansu a kuma amsa su. Wannan ma shine abin da ma'aikatar cikin gida ta taraiya tayi alkawari. Ko da shike hakan yana da kyau, amma bai kamata neman amsa wadannan tambayoyi ya zama al'amari na siyasa ba. Aiyukan da aka gano yanzu na kashe kashe da hare-hare, wajibi ne su shiga tattaunawar da ya kamata ayi, game da zaman baki a Jamus, musamman tsakanin al'ummar kasar.

Jam'iyar yan Nazi ta NPDHoto: picture alliance/dpa

Yanzu dai kusan shekaru 20 kenan tun da yan Nazi suka jefa bama-bamai a wasu gidaje biyu na iyalan Turkawa agarin Mölln, abin da a kasa baki daya har ma da kasashen ketare ya kawo bata suna da zubewar mutuncin Jamus. Kashe-kashen da aka gano su yanzu, sun nuna cewar har yanzu batun kyamar baki al'amari ne dake da gindin zama a kasar ta Jamus. A wasu yankuna na gabashin Jamus yan Nazi su ke fadi-aji, sukan kuma kwatanta kauyukan su a matsayin yantattu ko kuma yankuna na yan kishin kasa. Wadannan yan Nazi sukan yi ta rera wakoki na kyamar baki da kawo barazana ga duk mai wani ra'ayi dabam, ko baki ne ko kuma masu ra'ayin neman canji. Ko da shike irin wadannan mutane ba sune suka fi rinjaye a yankin ba, amma suna samun damar tafiyar da aiyukan nasu ne saboda rinjayen mazauna yankin sun ja bakin su sun rufe.

Duk da shekaru masu yawa da Jamus tayi a matsayin kasar dake karbar baki yan ci-rani, amma ra'ayoyi na kyamar baki har yanzu suna da gindin zama a kasar, ko da shike wnanan al'amari ne da ya sabawa abubuwan dake kunshe a tsarin mulkin Jamus. A ra'ayin masu kyamar bakin, dan ci rani, ko kuma bako, shine bisa al'ada yake da laifin duk mummunan abin da ya sami Jamus, saboda haka shi ya kamata a gwada karfi a kansa. Musamman saboda basa cin gajiyar bunkasar tattalin arzikin kasa, kamar marasa aikin yi, sukan dora laifin halin da suka shiga ne a kan baki. Yanzu haka yawan baki dake zaune a Jamus sun kai miliyan bakwai ko kuma kashi 10 cikin dari na al'ummar kasar baki daya. Ba ma saboda wadannan mutane miliyan bakwai ba, amma tsarin mulkin Jamus ya tanadi cewar wajibi ne a kawo karshen aiyukan yan Nazi tun daga tushen sa.