Abin da ya faru ya tuna min da watan Aprilu 2011, inda wancan lokacin sa'o'i gabanin fara zabe hukumar INEC ta dage zaben da kwananki biyu. Dalilin da aka bayar wancan shekarar ma dai kamar a bana hujja daya aka bayar na cewar kayayyakin zabe ba su kai ga isa a duk sassan kasar ba. A lokacin kowa ya rude, sai dai daga karshe an yaba wa shugaban hukumar Attahiru Jega da cewar matakin da ya dauka na dage zaben ya yi ma'ana.
Haka zalika a shekara ta 2015 Jega ya sake dage lokacin gudanar da zaben. Bayan da jami'an tsaro suka bashi shawarar cewa bisa rikicin boko haram da ya yi kamari ba za su ba da tabbacin yin zabe cikin lumana ba. Don haka INEC ta dage zaben da makwanni shida. a wancan lokacin a yi ta guna-gunin, amma a karshe aka gudanar da zabe na tarihi inda karon farko a tarihin Najeriya jam'iyyar adawa ta kada gwamnati mai ci, abin da ya dora Shugaba Muhammadu Buhari kan mulki.
Shin ko 'yan Najeriya na iya gamsuwa da wannan matakin dage zabe cikin dare daya. Daya dai sun kasa hakura, domin a shafukan sada zumunta an yi rabuta kana ko kan tituna mutum zai ji jama'a na cewa Allah wadai. Hukumomi na mai da kasarmu abun dariya. Sai kuma batun jita-jita da yarfe tsakanin masu mulki da 'yan adawa, yayin da 'yan adawa ke cewa jam'iyyar APC ce ta shirya makudin zabe, su kuwa masu mulki na cewa ai PDP ce ta saye hukumar zabe don a yi mata yadda take so.
A matsayin dan kallo mutum sai ya rasa me zai ce kan wannan lamarin domin har yammacin Juma'a hukumar zabe na cewa sun shirya tsab don samar wa Najeriya sahihin zabe. Tun makwanni akwai alamar shirin hukumar zabe na tafiyar hawainiya, don haka ba wani babban mamaki ba ne da jin labarin dage zaben.
To shin wa zai yi asara a wannan dage zaben, a tsari irin na Najeriya, komai abu ne da ka iya faruwa domin suna da wata siyasa mai matukar sarkakiya. A zahiri dai wata kila a cewa babbar jam'iyyar adawa ta PDP ita ce ke da asara domin ta fidda kudi na biyan wakilanta da za su kula da zabe a fadin kasar, yayin da a bangarenta APC mai mulki wannan asarar tana da sauki kasancewa suna kan mulk domin dama jihohi da suke mulki za su ba da kudin aiki.
Tsaka mai yuwa.
Yayin da wasu 'yan Najeriya suna dora laifi kan shugaban hukumar zabe Mahmood Yakubu da wannan rudu, amma wasu na ganin mutumin dake da babban laifi shi ne shugaba Muhammadu Buhari. Koma me ka iya biyo baya, a Najeriya a kan shiga irin wannan rudu amma daga karshe sai ka ga komai ya tafi salun alun.