Ko da yake har yanzu ba a baiyana sakamakon zaben shugaban kasar Kenya a hukumance ba, amma babu shakka nasarar da shugaba mai ci Uhuru Kenyatta ya samu ta haifar da fargaba. Sai dai muhimmin batu yanzu shi ne kada baiyana sakamakon zabe ya tada sabon rikici a fadin kasar, inji Andrea Schmidt shugabar Sashen Swahili na DW. Andrea Schmidt dai ta fara ne da cewa zaben ya kasance wani gumurzu tsakanin tsoffin masu adawa da juna a fagen siyasar kasar Kenya. Uhuru Kenyatta dai dan shugaban kasar Kenya na farko, shi kuma Raila Odinga da ne ga mataimakin shugaban kasa na farko. Kenyatta na kawancen jam'iyyar Jubilee ya lashe zabe. Shi kuma tsohon Firaminista Raila Odinga dan takarar sabon kawancen na NASA ya sha kaye. Wannan kuwa shi ne takarar Odinga karo na hudu, mai shekaru 72 hakan na zama damarsa ta karshe a kokarin neman darewa kan kujerar shugabancin kasar. Sai dai tuni ya nuna shakku ga sakamakon zaben, kamar yadda ya yi a zaben da ya gabata, inda a lokacin ya tafi kotu amma ya sha kaye. A dangane da fargabar barkewar tashin hankali da yawa daga cikin 'yan kasar Kenya sun fice daga manyan garuruwan kasar.
Raila Odinga ya yi zargin tabka magudi
Tun a lokacin yakin neman zabe Odinga ya ce ba zai amince da sakamakon zaben ba matukar ya fadi. Yanzu ya jaddada wannan matsayin yana mai zargin an tabka magudi kuma an yi kutse a na'urar hukumar zabe. Ya ce a wata cibiyar zabe ta sirri ta 'yan adawa akwai shaidun bayanai cewa shi ne ya lashe zaben. Wannan furucin ka iya angiza kabilun kasar da 'yan adawa su farma juna. Sai dai ya kamata 'yan sanda su nuna dattako ta yadda za su tinkari masu bore. A Kenya ana zargin jami'an tsaro da yawaita cin zarafin jama'a da ma yi wa mutane kisan ba gaira ba dalili. Ga misali a daren da aka gudanar da zaben an hallaka mutane da yawa a wasu yankuna na kasar. Da ma tun gabanin a gudanar da zaben kungiyoyin farar hula da majami'u da kafafan yada labaru sun sha yin kira da a kwantar da hankali a nuna halin ya kamata, kasancewa har yanzu 'yan kasar na tune da rikicin bayan zaben shekarar 2007 da ya yi sanadiyyar rayukan mutane fiye da dubu daya sannan aka kori wasu dubbanne daga matsugunansu. Bai kamata a sake maimaita wannan ta'asa ba.
Fargabar barkewar rikici
Hatta a kasashen duniya ma ana nuna damuwa game da sake rura wutar rikici a Kenya. Tsohon shugaban Amirka Barack Obama wanda mahaifinsa dan Kenya ne ya yi kira ga 'yan kasar da kada su bari a angiza su su farma juna. Shi ma babban sakataren Majalisar dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira ga 'yan kasar da su kai zuciya nesa.Shi ma Odinga da ke kiran kansa dan kishin kasa dan demokuradiyya bai kamata ya angiza magoya bayansa ba, yana iya garzayawa kotu don neman a tabbatar da sahihancin sakamakon zaben. Wanzuwar zaman lafiya a Kenya dai na da muhimmanci ga yankin gabashin Afirka baki daya. Ita ce babbar mai yaki da kungiyar Al-Shabab ta Somaliya. Su kuma kasashen da ba su da iyaka ta teku a yankin tsakiyar Afirka irinsu Yuganda da Sudan ta Kudu da Ruwanda da Burundi sun dogara da hanyoyin sufuri na Kenya wajen jigilar muhimman kayayyakin masarufi.
A wa'adin mulkinsa na farko, Kenyatta ya yi aikace-aikace masu yawa na samar da ginshikan tattalin arziki da hasken wutar lantarki da suka ciyar da kasar gaba. Sai dai a lokaci daya kuma kasar ta fada cikin badakalar cin hanci da rashawa da karin gibi tsakani talaka da mai kudi da kuma matsalar yawan yaje-yajen aiki. To ke nan da jan aiki a gaban shugaban, musamman na kirkiro da aikin yi ga matasa, ya kuma tabbatar ko wane dan kasar ta Kenya ya ci moriyar bunkasar tattalin arzikin kasa da daidaita farashin kayan abinci da daukar kwararan matakan yaki da rashawa. Babu tabbas ko shugaban zai iya yi wadannan ayyukan kasancewa ya kasa yi a wa'adin mulkinsa na farko. Fata dai shi ne al'ummar Kenya za su cire batun kabilanci a cikin lamuran zabe, su ba wa masu tasowa wani sabon ruhi na siyasa.