1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhi kan gasar cin kofin Afirka a Angola

February 1, 2010

Menene makomar manyan filayen wasannin da aka gyara domin gasar cin kofin Afirka a biranen Angola?

Filin wasan TundavalaHoto: AP

Acikin makonni uku da suka gabata ƙasar Angola ta kasance cibiyar da aka gudanar da gasar cin kwallon kafa ta Afirka. Angola dai ta so nunawa Duniya cewar itace ƙasar Afrika dake samun bunkasuwar tattalin arziki, zamantakewa, kuma mai masaukin baƙi na wannan muhimmin gasa na ƙasasahen Afirka.

Wasannin kwallon ƙafa dai na bukatar cikan filin wasa da 'yan kallo, wanda hakan zai kuma kayatar da wasan baya ga ƙarfafa gwiwar 'yan wasan. Domin rashin cikan mutane a filin wasa da 'yan kallo zai iya kashe ƙwarin gwiwar su kansu'yan wasa. To wasan na ƙasar Angola dai ya kasance mai kashe jiki, saboda duk da cewar akwai manya-manyan wuraren da aka tanada an fuskanci matasalar karancin mutane da zasu cika dubban kujeru dake filayen.

Ko a wasannin zagayen kusa da na karshe da aka buga tsakanin ƙasashen Nigeria da Ghana, da kuma Algeria da Masar, babu abunda ya mamaye filayen face 'yan jarida da Na'urorin aikinsu, ayayinda mutane kalilan kake iya gani masu goyon bayan 'yan wasa, waɗanda ke cikin shaukin murna da annashuwa da rewa wakokin karfafa gwiwa ga 'yan wasan. Ko a wasan karshe da akayi jiya tsakanin Masar da Ghana a birnin Luanda, dubban kujeru sun kasance fayau babu mutane. Launukan Ja da ruwan kwai dake ɗaukar ido a wurin wasan na Luanda a jiya, ya kasance launukan kujerun amma ba na tutocin Masar ko Ghana da suka buga wasan na karshe ba.

Filin wasan LuandaHoto: AP

Abunda yafi muni ma tun a lokutan wasannin farko. A ranar da akayi wasa tsakanin Malawi da Algeria, mutane 'yan kalilan ne suka bayyana a filin wasan na Luanda, kana a ranar da Angola zata yi wasa, sai da jami'iyyar MPLA mai mulkin kasar tayi kira ga jama'a dasu bayyana a filin wasan domin ƙarawa 'yan kwallon karfin gwiwa.

A kwai dalilai da dama da za a iya dangantawa da wannan matsalar, masu hannu da shunin ƙasar ta Angola dake da sukunin sayen tikitin shiga wuraren wasannin, sun guji hargitsi da ka iya ɓarkewa kamar yadda aka saba a lokutan fitattun wasannin kwallon kafa.

A maimakon haka dai sun gwammace shiga motocinsu masu tsada suna tafiya sayayya ko kuma zuwa bakin ruwa ko kuma fitattun wuraren shakatawa na birnin na Luanda.

A hannu guda kuma dubban mutanen dake muradin zuwa kallon wasannain basu da sukunin sayen tikitin shiga filayen wasannan saboda tsadarsa. Kazalika suna 'yan ƙasashen wajen sun ki zuwa Angolan domin bawa idanunsu abinci dangane da wasannin na cin kofin Afrika.

An danganta Angolan dai da kasance ɗaya daga cikin birane mafi tsadar Rayuwa a Duniya.

Shirya gasar kwallon kafa kowane irin nedai yana cin makuddan kudade,gwamnatin Angola ta kashe kimanain dala biliyan guda na Amurka, wajen tsara matakai guda huɗu na wasannin, da kuma kayyakin ada ake bukata, a kasar datafi kowace mace-macen kananan yara kafin su cika shekaru biyar da haihuwa.

Yara kananaHoto: AP

Me yasa gwamnati bata kashe waɗannan makuddan kuɗaɗen akan inganta cibiyoyin kiwon lafiya, ko samar da ruwa ko kuma tabbatar da muhalli mai tsabta ba musamman a unguwannin birnin na Luanda dake fama da matsaloli?

Tun daga tushe dai, an fara gasar ne cikin rashin jin dadi, sakamakon harin da kungiyoyin tsiraru na Cabinda suka kaiwa 'yan wasan kwallon kafa ta Togo wanda yayi sanadiyyar janyewar kasar daga gasar cin kofin Afrikan na wannan karon.

Bisa dukkan komai dai ana iya cewar gasar a maimakon cigaba tamkar koma bayace ga harkokin siyasar Angola. Menene matsayin manyan filayen wasannin da yanzu ke girke, da kuma kundin tsarin mulkin ƙasar, ayayinda a hannu guda kuma 'yan adawa na cigaba da kasancewa a kurkuku.

Mawallafiya: Zainab Mohammed

Edita: Mohammad Nasir, Awal