1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhi kan harkokin siyasa a Kenya bayan zaɓen shugaban ƙasa

December 31, 2007

Rahotanni sun ce mutane sama da 100 aka kashe tun bayan bayyana sakamakon zaɓen

Magoya bayan Odinga suna ƙone-ƙone a NairobiHoto: AP

Tare da wani rinjaye da bai taka kara ya karya ba al´umar Kenya sun sake zaɓen shugaba Mwai Kibaki don yayi ta zarce yayin da shugaban ´yan adawa Raila Odinga ya sha kaye. Da farko zaɓen wanda ya zama tamkar wani abin misali, daga baya an shiga cikin ruɗami sakamakon jinkirta bayyana sakamakonsa. Magoya bayan jam´iyar ODM ta Odinga sun zargi gwamnati da maguɗin zaɓe. Sannan ita kanta hukumar zaɓe da masu sa ido na ƙasa da ƙasa sun ce an aikata ba daidai ba, inda aka hana wakilan tawagar ganewa idonsu yadda aka ƙidaya ƙuri´u a wasu mazaɓu. To amma duk da haka an rantsad da Mwai Kibaki jim kaɗan bayan sanar da sakamakon zaɓen a jiya lahadi.

Zab´ɓen wanda ke zama irinsa na biyu a tafarkin demoƙuraɗiyya a Kenya shi ne kuma irinsa na farko da aka samu kusantan yawan kuri´u a tarihin ƙasar. Har zuwa ƙarshe an yi ta yin kafaɗa da kafaɗa tsakanin shugaba mai ci Mwai Kibaki da mai ƙalubalantarsa Raila Odinga, inda da farko Odinga ya kasance kan gaba. Da farko dai yawan mutane sama da kashi 70 cikin 100 da suka kaɗa kuri´unsu ya kasance wata kyakkyawar alama ga mulkin dimoƙuraɗiyyar wannan ƙasa dake gabashin Afirka inda ƙabilanci ke taka rawa a harkokin zaɓe. Munanan tashe tashen hankula tsakanin ƙabilu daban daban a faɗin ƙasar bayan sanar da sakamakon zaɓen, sun sa ana nuna damuwa game da ɗorewar zaman lafiya a ƙasar ta Kenya.

Kibaki wanda ya maye gurbin tsohon shugaban mulkin kama karya Daniel Arap Moi a shekara ta 2002 ya kasance wani babban abin fata. Ci-gaban da aka samu a lokacinsa ya haɗa da bunƙasar tattalin arziki da ba da ilimin firamare kyauta. Ya taimaka wajen ciyar da mulkin dimoƙuraɗiyya a ƙasar gaba. A ƙarƙashinsa Kenya ta yi fice wajen kyautata ´yancin ´yan jarida. To sai dai a wa´adin farko na mulkinsa shugaba Kibaki ya gaza wajen yaƙi da cin hanci da rashawa da rage talauci da miyagun ayyuka wanda ya lashi takobin yaƙarsa

Kibaki dai ya lashe wannan zaɓe a ƙarƙashin tutar jam´iyar ƙawance ta PNU, to amma ministoci da dama sun rasa mukamansu domin ba a sake zaɓensu a majalisar dokoki ba. Hakan dai zai tsananta aikin gwamnati ƙarƙashin jagoranci Kibaki. Duk da haka dai bai kamata sabuwar gwamnati ta yi watsi da bukatun al´umma ba. A wa´adin mulkinsa na biyu kuma na ƙarshe dole ne Kibaki ya yiwa kundin tsarin mulkin ƙasar kwaskwarima, dole dukkan ´yan kasar su ci gajiyar bunƙasar tattalin arzikinta sannan dole ne kuma ya yaƙi matsalar cin hanci don ya samu amincewar talakawa. To amma abu mafi muhimmanci yanzu shi ne a warware zargin tabƙa maguɗin zaɓe, ´yan ƙasar sun kwantar da hankalinsu kana kuma a kawo ƙarshen rikicin ƙabilanci nan take.