Sharhi kan nada sabbin ministoci a Najeriya
July 10, 2014Cikin wadannan ministoci akwai ministan Ilimi Malam Ibrahim Shekarau, tsohon gwamnan jihar Kano da Stephen Oru, minista a ma'aikatar kula da harkokin Niger Delta da Abdul Bulama, minista a ma'aikatar kimiya da fasaha sai kuma Clement Adebayo Adeyeye, karamin ministan a ma'aikatar ayyuka.
Babban abinda za a tsammaci gani dai bai wuce irin sauyi da wadannan sabbin ministoci za su samar a ma'aikatun da aka basu ba, lamarin da wasu ke ganin cewa babu wani sauyi da za su samar kamar yadda Dr. Aminu Umar malami a Kwalejin Fasaha ta Kaduna ke cewa.
"Ka san nadin minista a Najeriya kamar dai cike gurbine, saboda ba wai dama ce ta cewa mutum ya fito ya yi aiki yadda ya dace ba, saboda kwarewarsa ko ya kwaci al'umma da wannan mukami da aka nada shi a kai. Siyasa ita ce kan gaba kafin tunanin abinda za'a yi wa mutane, cikin nade-naden da ake wa mutane. Idan ka duba kasashen duniya kafin abai wa mutum mukami ya rike sai an ga kwarewarsa kafin siyasa ta biyo baya, to amma ba haka abin yake ba a kasar tamu. Tana yiwuwa suna da kwarewar yadda ya dace amma siyasa ba za ta bari su yi aikin ba yadda ya dace"
Shi kuwa a nasa ra'ayin mai fafitikar kare hakkin bil Adama kuma lauya mai zaman kansa Dahiru Ibrahim Yakasai, cewa ya yi dole ne sabbin ministoci ga misali tsahon gwamnan Kano, ya sauya salo a irin yadda yake rike mukami, ganin irin gwamnatin da zai yi wa aiki.
"Wannan gwamnati ba kamar sauran gwamnatoci bane da ake bawa mutum wuka da nama, wajen gudanar da ayyukan da yake ganin sun dace, kuma ayyuka da suka dace da tsarin mulki. Zai fiskanci wannan matsala sannan kuma shi mutum ne mai sanyi ba mai zafi ba. Najeriya kuma na bukatar mutum mai hanzari, gaskiya yana da babban kalubale, dole ne ya canza, ya san cewa wannan kujera da aka ba shi, ba wai shi aka bawa ba, arewacin kasar aka baiwa"
Da dama dai masharhanta na kallon bada wadannan kujeru ga ministocin daga arewacin kasar, da cewa yana alaka da bukatar neman su share wa shugaba Goodluck Jonathan hanya, a kokarin da ya ke yi na maido da kimarsa a yankin, gabannin zaben kasar na badi.
Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Usman Shehu Usman