sharhi kan raayoyin manazarta kan Amurka da Iran da rikicin yakin gabas ta tsakiya
July 20, 2006Manazarta kan harkokin siyasa na na yankuna,sunyi nuni dacewa Amurka na iya amfani da rikicin dake gudana tsakanin Hizbollah da Izraela,wajen afkawa Iran da karfin soji.
A yanzu haka dai masu tsattsauran raayi na Izraela na cigaba da bayyana cewa Iran ce ta ingiza wutan harin day an hizbollah suka kai kan iyakar Izraela da Lebanon a ranar 12 ga wata,kuma bisa dukkan alamu mafi yawan mutane sun amince da hakan ,ganin yadda ake yayata wannan raayin a kafofin yada labaru,dama wasu yan siyasa masu fada aji.
Gregory Gause dake koyarda darasi kan harkokin yankin gabas ta tsakiya a jamiar Vermont,yana mai raayin cewa wannan shine mafarin makamancin abunda ya faru tsakanin harin kunar bakin wake a amurka a ranar 11 ga watan satumban 2001,da kuma yakin kasar Iraki.
Ya bayyana cewa ayayinda masu raayin mazan jiya ke jagoranci a yayin gabatar da raayoyinsu a wancan lokaci,raayi yazo daya tsakanin yan siyasan Amurka nacewa,kaddamar da yaki akan Iraki nada matukar tasiri wajen sake yin gyara a yankin gabas ta tsakiya,domin kare sake aukuwan yanayi kamasr na 11 ga watan satumba.
Mr Gregory yace a wannan can lokacin wannan raayin ya samu goyon baya daga bangaren masu sassaucin raayi kan lamuran rayuwa.Kuma aganinsa,tarihi zai sake maita kansa cikin yan shekaru ,ko ma watanni masu gabatowa a dangane da afkawa Iran da karfin soji.
Ko shakka babu,domin tabbatar da wannan has ashen,a ranar talata ne majalisar dottijan Amurkan baki daya,ta amince da bawai kudurin dake marawa Izraela baya,adangane da hare haren da take kaiwa Lebanon da zirin Gaza a yankin palasdinawa kadai ba,amma harda kira ga shugaba George W Bush daya daya kakabawa Iran da Syria takunkumi na diplomasiyya dana tattalin arziki.Kudurin da a hannu guda kuma akesaran yan majalisar wakilai suma zasu amince da ita.
Kafin a kawo ga wadannan rigingimu dai,Tehran tasha zargin Amurka da hannu dumu dumu cikin rigingimun yankin na gabas ta tsakiya.
Bugu da kari bayan tarihinta na marawa yan Hizbollah baya,Tehran na kuma marawa kungiyar Hamas baya,duk da wadanda ke zaune a Damscus,wadanda ake zargi da sace sojin Izraela guda a watan daya gabata,dalili kuma daya haifar da somame da izraelan takai zirin Gaza.
Jaridar Newyork Times a makon daya gabata ta gabatar da sharhin Thomas Friedman,wanda ke nuni dacewa ya dace duniya tasa halin da ake ciki a dangane da wadannan rigingimun.Domin bisa dukkan alamu,ana neman tuge tushen democradiyya daya fara samun gindin zama a Lebanon da Iraki da kuma yankin palasdinawa.
Kuma ga alamu ana zargin Iran ne da ingiza yan Hizbolla da harin kan iyaka na ranar 12 ga wata,wanda kuma ya haifar da rikicin wutan jeji dake neman cinya yankin gabas ta tsakiya baki daya,musamman tsakanin Iran din da Amurka dake neman daukan matakan ladabtarwa akan shirin nuclearn na Tehran.
To sai dai ga mafi yawan manazarta da kwararru ta fanning siyasan duniya,Amurka ce ummul abaisin dukkan waddan rigingimu dake dada yaduwa a yankin gabas ta tsakiya.Suna ganin cewa baya ga miyagun tsare tsare,Amurkan kamar yadda tayi kuskure da yakin data jagoranta a Iraki,tana cigaba da bada cikakken goyon bayanta wa Izraela a wadannan illoli datake cigaba da haifarwa a yankin baki daya.