1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tasirin siyasar ubangida ko akasinsa

December 15, 2023

A wani abin da ke iya kai wa ga barazana a fagen siyasar Najeriya, ana kallon karuwar rikicin gida mai zafi a tsakanin ubangida da yaransu cikin fagen siyasar kasar.

Nigeria I Ezenwo Nyesom Wike
Hoto: Getty Images/AFP/Y. Chiba

Kama daga Awolowo da Akintola tun daga farkon fari, ya zuwa Aminu Kano da Abubakar Rimi da ke zaman dan cikin gida na siyasa daga baya, tarrayar Najeriya ta dauki lokaci tana kallon rikici a tsakanin ubangida na siyasa da masu gado a cikin mulkin dake da zakin gaske.

Ana kuma kallon ta'azzarar gwagwarmayar neman ikon ko dai a jihar Anambra inda Chris Ngige ya juya baya ga ubangidansa Chris Uba, ko kuma can a Kano inda Ganduje ya cewa Kwankwaso baka isa ba.

Hoto: next24online/NurPhoto/picture alliance

Ita ma jihar Legas ta harbu da rikici tsakanin shugaban kasar da ke ci yanzu Bola Ahmed Tinubu da babban yaronsa Akinwumi Ambode

Karin Bayani: Rikicin siyasa na ta'azzara a Jihar Rivers

Ko a halin yanzu ma fagen siyasar kasar na kallon wani sabon rikicin tsakanin Similaye Fubara da ke mulki a Jihar Rivers da tsohon gwamnan jihar Nyesom Wike da ya yi nasarar dora shi kan karagar mulkin jihar. Rikicin kuma da sannu a hankali yake kara fidda maita fili, cikin gidan na siyasa inda ake fadin dan talaka, amma kuma ake kokarin nuna yi don amfanin kai.

Hoto: Kwankwasiyya official Foto, Kano Nigeria

Abubakar Sani Bello dai na zaman tsohon gwamnan Niger da kuma ya mika mulki a cikin watan mayun da ya shude, ya kuma ce masu laifi a cikin gwagwarmayar neman ikon na zaman tsofaffin gwamnonin da ke da bukatar cin tudu biyu.

Karin BayaniNajeriya: Zaben shugabannin manyan jam'iyyun siyasa a jihohi ya bar baya da kura

Kama daga masu kirari na kauce wa akidar gado, ya zuwa masu kiran saba wa alkawari dai, dalilai iri iri na bayan rigingimun da ke da babban burin kai karshen tasiri na siyasar da kila ma babakere na abokan rikicin

Hoto: Salihi Tanko Yakasai

To sai dai kuma rikicin na dada tasiri ga makomar dimukuradiyyar kasar da ke da bukatar hidima, amma kuma ke kallon fada na kaiwa bakin hadama. Koma ina batun nada mai gadon ke shirin zuwa cikin yamutse hazon siyasa a cikin tarrayar Najeriyar, tsarin yana iya zama zakaran gwajin dafin sauya da dama cikin batun ginin kasa mai tasiri.

Faruk BB Faruk na sharhi kan batun siyasa, kuma yace tsarin ya taimaka wa kasashen irin su Rasha wajen dada samun karfi da kila ma tasiri ga rayuwar al'ummarsu in an kauce wa batun tara arziki a cikinsa. Ko bayan kokarin tada bukata ta rayuwa dai, a mafi yawancin lokaci cikin fagen siyasa ta kasar na da babban burin kare dukiyar wasoso daga aljihun gwamnati.