1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhi: Yadda Turai ke kallon kisan bakar fata a Amirka

June 2, 2020

A sharhin da ya rubuta kan martanin da ake mayarwa a Turai bayan kisan bakar fata George Floyd a Amirka, Chiponda Chimbelu na tashar DW, ya yi kira ga Turai da ta kara azama a yaki da wariyar launin fata.

Chiponda Chimbelu DW Journalist
Chiponda Chimbelu dan jarida a DWHoto: DW/U. Beck

Ba na cikin kwanciyar hankali wai don ina zaune a Jamus, inji dan jaridar tashar DW Chiponda Chimbelu, a sharhin da ya rubuta kan martanin da ake mayarwa a Turai na kisan bakar fatar Amirkar nan, George Floyd da ake zargin wani sanda a Amirka da aikatawa. Chiponda ya kara da cewa wannan lokaci ne da ya kamata nahiyar Turai ta sake yin karatun ta natsu kan matsalolin wariyar launin fata a nahiyar.

Chiponda Chimbelu na tashar DW ya ce kisan George Floyd na zama lokaci daya tilo da abokansa da dama suka tuntube shi game da kisa da ke da nasaba da wariyar launin fata. Amma abin da ya fi daukar hankalinshi shi ne tambayar da wani abokinshi ya yi masa cewa ko yana farin ciki da ba ya Amirka yanzu?

Chiponda ya ce gaskiya hankalinshi ba shi kwance wai don yana Jamus. Ya ce yana cikin fushi yana kuma jin takaici, domin shekaru da dama ana yi wa bakar fata kisan gilla wasu a hannun 'yan sanda. Kuma kisan George Floyd na yi mana tuni cewa rigingimu na wariya a wasu lokuta ka iya kai ga asarar rai.

Hoto: picture-alliance/AP Photo/M:.Schreiber

Boren da ake yi a biranen kasar Amirka da yanzu a wasu manyan birane kasashen Turai na nuni karara fusata da takaicin da bakar fata ke ji na wariya a hannun hukumomi da wasu ma'aikatu na gwamnatoci. Kar kuma mu yi tunanin cewa matsala ce ta Amirka kadai. Kyamar bakar fata ta zama ruwan dare a kasashen yamma.

A 2011 an yi zanga-zanga a London bayan kisan Mark Duggan, bakar fata da 'yan sanda suka harbe har lahira. A 2005 zanga-zanga ta barke a Faransa sakamakon mutuwar wasu matasa biyu bakar fata lokacin da suke tserewa 'yan sanda. A shekarar kuma wani dan kasar Saliyo, Oury Jalloh ya mutu a tashin gobara a gidan wakafi a Dessau da ke nan Jamus. 

Cikin sauki wasu Turawa na iya kallon abubuwa da ke faruwa a Amirka su ce ba za su faru a Turai ba, sai dai bakar fata a Turai ba sa cikin wani yanayi na gata. A garesu wariyar fata tana nan daram a Turai duk da gaskiyar cewa ba safai azabar da suke sha a hannun 'yan sanda ke daukar hankalin jaridu ba. Bisa wannan dalili ne kisan George Floyd ya janyo bore hatta a wajen kasar Amirka. 

Hoto: picture-alliance/dpa/H. Schmidt

Abin bakin ciki rahotanni a kafafen yada labarai da manhajojin koyarwa a makarantu a kasashen yamma sun gaza yin wani abin kirki na sauya tunanin mutane kan yadda suke kallon batun launin fata. A 2017 wani shirin gwamnatin Jamus kan yaki da wariyar fata ya ce bakar fata na daya daga cikin rukunan al'ummomin biyar da ke da babbar kasadar fuskantar wariya. Sai dai wannan bayani ya zo ne shekaru da dama bayan matsin lamba daga Kwamitin Majalisar Dinkin Duniya mai fafatukar kawar da wariyar launin fata, da ya sha zargin gwamnatin Berlin da rashin yin wani katabus na yaki da bambancin launin fata.

Wai don ba ma samun labaran asara rai, ba ya nufin babu matsalar wariyar fata a Turai. Za mu iya nuna zumuncinmu wajen bayyana sunan George Floyd muna kuma tattauna batun rashin adalci na wariyar launin fata da yadda hakan ke shafar rayuwar mutane a cikin al'umma domin mu magance shi.