1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhi kan kalubalen da Mali ke ciki

DW Kommentarbild Mouhammadou Awal
Mouhamadou Awal Balarabe
August 21, 2020

Duk da adawa da juyin mulki da kasashen ketare suka nuna, 'yan adawa da 'yan farar hula a Mali sun yi alkawarin yin aiki tare da gwamnatin mulkin sojan kasar.

Shugaban gwamnatin mulkin sojan Mali Kanal Assimi GoitaHoto: Getty Images/AFP/M. Konate

Bangarorin biyu sun sanar da gudanar da gangami a wannan Jumma'a domin nuna farin cikinsu game da nasarar da suka samu a kan shugaba Ibrahim Boubacar Keïta. Sai dai a sharhinsa da ya rubuta, Mouhamadou Awal Balarabe edita a sashen Hauasa na DW, ya ce akwai matsaloli da ya kamata su magance idan suna son su fitar da kasar Mali daga mawuyacin halin da take ciki. Juyin mulkin kasar Mali bai kasance wani abin mamaki ba, duba da rikice-rikice da suka mamaye wannan matalauciyar kasa ta yammacin Afirka. Ba ta da ingantaccen tsarin tattalin arziki, babu kwanciyar hankali a aksar, babu ci gaban siyasa ballantana talaka ya ga ayyukan raya kasa a tafin hannunsa.

Gagarumin kalubale

Ko da sabon shugaban mulkin sojar kasar, Kanal Assimi Goita ya fahimci cewa akwai jan aiki a gabansu wajen fitar da Mali daga mummunan halin da take ciki, lamarin da ya saka shi cewa ba su da '''yancin yin kuskure." Ko da yake ya bayyana aniyarsa ta kafa harsashin sabuwar Mali, amma kuma hanyar da zai bi wajen cimma buri na cike da tarnaki. Sai dai a fili yake cewa al'umma sun gaji da gafara sa ba tare da ganin kaho ba, duba da juyin mulkin shekara ta 2012 da aka yi da bai kawo wani ci-gaba ba, in ban da share wa hambararen shugaba hanyar darewa kan kujerar mulki bisa tafarkin dimukuradiyya. A cewar Mouhamadou Awal Balarabe editan sashen Hausa na DW, abu daya ta ya fito fili a Mali shi ne, kusan dukkanin fannoni na bukatar agajin gaggawa, sakamakon yadda al'amura suka rincabe. Idan dai ana so a fitar da A'i daga rogo, sai an aza harsashin ginin sabon tsarin doka da oda, wato samar da kotu mai adalci ba mai bangaranci ba.

Mouhamadou Awal BalarabeHoto: DW/A. Salisu

Akwai kuma bukatar samar da cibiyoyin gwamnati kama daga asibitoci zuwa makarantu a duk fadin kasar, baya ga samar da tsaro. Sai dai wannan ba zai samu ba sai da taimakon makwabciyar kasa Aljeria, wacce sojojinta ke taka rawa wajen tayar da hankalin a arewacin Mali, ta hanyar amfani a wasu lokutan da wasu kungiyoyin ta'adda. Wannan na nuna cewa tabbas ba za a iya yin yaki da ta'addanci ba, ba tare da karfafa horon aikin sojojin Mali da kuma kwance damarar 'yan bindiga ba, wadanda yawaitar su ne sillar raunin da gwamnatin ta fuskanta. Ayar tambaya a nan ita ce, gwamnatin mulkin sojan Mali za ta iya shirya tattaunawa da dukkan bangarorin siyasa da farar hula da masu gwagwarmaya da makamai domin gano bakin zaren dora kasar kan turba madaidaiciya?

Hada hannu waje guda

Shi dai sabon shugaban mulkin sojan ya riga ya ci nasara, inda gamayyar kungiyoyin adawa ta M5-RFP ta ce a shirye take ta yi aiki tare da shi. Sai dai Kanar Assimi Goita ya kwana da sanin cewar Mali ba za ta iya farfadowa ba matukar ba a samar da sabon jini da ke da tunani iri daban a fagen siyasa ba. Sannan kuma ya wajaba a kaddamar da yaki da cin-hanci da rashawa gadan-gadan, tare da neman ceto madugun ‘yan adawar kasar Soumaila Cissé wanda 'yan bindiga suka sace tun cikin watan Maris. A hakikanin gasakiya ma dai, daga yanzu babu wani abin da za a iya yi a Mali ba tare da tabarrukin Imam Mahmoud Dicko da ma sauran malaman addini da ke da karfin fada a ji ba

Imam Mahmoud DickoHoto: DW/K. Gänsler

Amma da kamar wuya a shawo kan wadannan matsaloli cikin hanzari, saboda Kanal Goita ba zai samu hadin kan kasashen duniya ba, wadanda suka yi Allah wadai da juyin mulkin tare da yin kira da a mayar da Mali kan tafarkin dimukuradiiya. Wannan dai na nuna cewa bukatun talakawan Mali sun sha bamban da na kasashen da ke matsa lamba. A wannan gabar dai, akwai bukatar fara kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali, idan ya so daga bisani a bai wa tattalin arziki damar murmurewa, kafin a shirya zaben da zai mayar da ita kan tsarin dimukuradiyya. Amma ba za a iya aiwatar da wannan tsarin ba tare da gudummawar kungiyoyin kasashe irin su ECOWAS da AU da EU ba, saboda Mali ba ta da wani ikon da zai ba ta damar karfafa tsarin kasar.

Ita kuwa Faransa da ta yi wa Mali mulkin mallaka kuma take ci gaba da babakere a kasar, tana da nata hakkin saboda tana yin harshen damo, inda take fifita matsayin kabilun Sahara, lamarin da ke mummunan tasiri wajen mayar da Mali tsintsiya madaurinki daya. Saboda haka dole ne ta kasance mai neman daidaita lamura tare da tallafawa, domin sabunta Mali da kawar da ta'addanci a yankin. Matukar dai Mali ba ta yi nasarar a kan wadannan kalubalen tare da shirya sahihin zabe ba, to za ta ci gaba da hangen dala, lamarin da zai sa talauci da tashin hankali su ci gaba da katutu a kasar.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani