1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bolibiya: Ruwa ya kare wa dan kada

November 12, 2019

Daga karshe kokarin cigaba da dawwama kan kujerar mulki, ta hanyar kiran sabon zabe ya ci tura. Shugaban Bolivia ya makara wajen yin martanin da ya dace biyo bayan zanga-zangar adawa na kasa baki daya.

Hoto: picture-alliance/dpa/EPA/M. Alipaz

Shugaban Bolibiya ya makara wajen yin martanin da ya dace biyo bayan zanga-zangar adawa na kasa baki daya, duk da  bayyanar alamu karara. Wannan shi ne ra'ayin Johan Ramirez dangane da halin da Bolibiya ta tsinci kanta ciki. Marubucin sharhin ya ce, shugaba Evo Morales na Bolibiya ya kasa fahintar rigingimu na siyasa da kasarsa ke fuskanta, wanda ke zama abun mamaki ga mutumin da ke kan karagar mulki tun daga shekara ta 2006.

Ba wai kawai bai fahinci cewar tauraronsa ya dusashe cikin sheakaru 14 na mulki ba, amma ya nuna cewar bai ma fahinci alamun kiyayya da ya ke fuskanta, irin kura-kuran da a siyasance ba'a cika yin afuwa akansu ba.Morales ya yi fatali da sakamakon zaben raba gardama da aka guudanar a shekara ta 2016, a lokacin da al'ummar kasar suka ki amincewa da yunkurinsa na yin ta zarce a karo na hudu. Wannan sakamakon shi ne alamu na farko da shugaban ya kasa fahinta. Sama da rabin al'ummar kasar suka nuna muradunsu na ganin a samu sauyi, kuma hakan a bun tsoro ne a demokradiyya.

Tsohon shugaban Bolibiya Evo Morales Hoto: picture-alliance/dpa/J. Karita

A maimakon ya yi kokarin renon wani dan takara a jam'iyyarsa ta 'yan gurguzu ta MAS, wanda watakila da hakan ne zai bai wa jam'iyyar ta su damar cigaba da rike madafun iko, sai ya samu damar sake yin takara a hukumance. Zanga zangar adawa da takararsa basu hana Morales janyewa ba, kasancewar ya lashi takobin lashe zaben, nasara a zagayen farko. Rahoton da gamayyar kasashen yankin Amurka suka gabatar a ranar Lahadi, na nuni da irin magudi da aka tabka. An bankado kura-kuran da murdiya irin wadanda ko a wannan kasa tasa ta masu tsattsauran ra'ayi, babu wanda zai lamunta.

Bayan zagayen farko na sakamakon zaben da ya bayyana Morales a matsayin wanda ya yi nasara, 'yan adawa suka bazama kan tituna domin nuna fushinsu tare da bukatar sake kidayan kuri'un. Batun da shugaban ya yi kunnen uwar shegu da shi. 'Yan kwanaki kalilan daga bisani, gangamin adawan ya kazanta, inda 'yan adawa suka nemi da a soke sakamakon zaben, domin gudanar da sabo. Nan ma shugaban ya toshe kunnuwansa. Kira-kirayen Morales ya yayi murabus daga shugabancin kasar ya cigaba da ta'azzara.

Johan Ramírez wanda ya rubuta sharhiHoto: DW

A ranar asabar, shugaban ya aike da sako wa al'ummar kasar, wanda a wannan karon ma, ke nuni da cewar bai fahimci halin da kasar ke ciki ba. Ya yi watsi da batun shirin kifar da mulki, ya yi jawabi game da nuna wariya tare da kira ga magoya bayansa dasu fito domin kare martabar gwamnatinsa.Duk da cewar ya yi kira da agudanar da zaman sulhu, bai sanya kwamitocin al'umma da a yanzu haka su ne jagororin a dawar kasar cikin tattaunawar ba. Bai yi la'akari da karfin iko da suke da shi na hada kan al'umma wuri guda ba. Kuskuren karshe da Morales ya yi a siyasance, shi ne na rashin sanin cewar 'yan adawar sun rikide zuwa wakilan al'umma masu fafutukar neman sauyi.

Kwatsam ranar Lahadi, Morales ya wayi gari da kiran a gudanar da sabon zabe, sanarwa da tazo a makare da wajen kwanaki 10. Lokaci ya kure masa, masu zanga zanga sun rigaya sun samu mazauni a kan tituna. Dole ne kawai Molarales ya kau domin bai wa Bolibiya damar bude sabon babi a siyasance.