1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhi: Ranar tuni da hadewar Jamus

October 3, 2018

Shekaru 28 bayan hadewar gabashi da yammacin Jamus, har yanzu an bar yankin gabashi a baya ta fuskar tattalin arziki. Sai dai akwai dalilai da dama bayan fannin tattalin arzikin a cewar Marcel Fürstenau na tashar DW.

Kofar Brandenburg mai tarihi a BerlinHoto: Reuters/F. Bensch

Marcel Fürstenau na DW ya fara sharhin nasa ne yana mai cewa: Za a iya bayyana Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a matsayin wacce ta fi cin moriyar sake hadewar Jamus din tare da jam'iyyarta ta CDU. Wacce aka haifa a birnin Hamburg amma ta girma a yankin gabashin Jamus (DDR) a wancan lokaci, ita ce ke mulkin kasar na tsahon shekaru 13, sai dai a yanzu abubuwa na tabarbarewa. Ko da shugabar gwamnatin wadda ke zaman guda daga cikin masu iko ba za ta ci gaba da yin alfahari da yankin gabashin Jamus din ba, wannan na zaman guda daga cikin dalilan da ya sanya aka fi jin tamkar ana nuna wariya ga yankin gabashin fiye da yankin yammacin Jamus din. A fili yake karara cewa Merkel na wakiltar siyasar da ta kasance ba ta ra'ayinta ba, duk da cewa da ita da su abu guda ne wajen sanin irin mulkin kama karyar da aka gudanar a baya. Tun bayan faduwar katangar Berlin gwamnati ke kokarin bunkasa yankin, sai dai ga wasu miliyoyin al'ummar yankin gabashin Jamus din ba ta sauya zani ba. Babbar matsala ita ce ta rashin aikin yi har yanzu.

Marcel Fürstenau na DW wanda ya rubuta wannan sharhiHoto: DW

Nasarar da suka cimma a rayuwarsu ta fuskar ci-gaba da bunkasar al'adu da tattalin arziki ta bare daya ce. Kafin cimma wannan nasara tilas a bi abubuwa a sannu da kuma tabbatar da daidaitonsu. Babu batun yin sauye-sauye a fannin tattalin arziki ko kuma wani gagarumin sauyi na siyasa da aka taba samu kawo yanzu a tsohuwar Tarayyar Jamus din. Yayin da a hannu guda yankin gabashin Jamus din ya fuskanci jajircewa cikin kankanin lokaci, abin da mutane da dama ba su yi na'am da shi ba. Sai dai ya taimaka gaya wajen gyara al'amura. Juyin-juya hali cikin lumana da aka gudanar a shekarun 1989 zuwa 1990 ya sanya mutane da dama da ba sa iya sayen wasu abubuwan bayan hadewar Jamus din da dama sun shawo kan wannan matsalar.

A bayyane yake karara dangane da batun sake hadewar Jamus din cewa: Albashin da ake biyan ma'aikata a yankin gabashin Jamus shekaru 28 bayan kawo karshen rabuwar kasar kaso 82 cikin 100 kacal na wanda ake biya a yammaci. Wanda ya dauki hakan a matsayin ci gaba lallai ya runtse idanunsa. Biyan kudi kadan ga wasu a aiki iri guda kuma alokaci guda na nufin mayar da su saniyar ware da rashin daraja su. Rashin biyan albashi mai kyau da kuma rashin biyan ma'aikatan da suka yi ritaya hakkokinsu da kuma sauran abubuwa na rashin adalci na da illa mai yawa ga rayuwa. Ga wadanda suka shekara 50 ko sama da haka, bambancin da ke tsakanin bangarorin biyu na da cin rai. Wannan matasala na ci gaba da haifar da runadani.

Angela Merkel a bikin ranar hadewar JamusHoto: Reuters/F. Bensch

Wani abu mai daure kai shi ne yadda masu fada a ji na yankin yammacin Jamus suka yi kaka gida a kusan dukkan bangarorin al'umma. Idan aka cire Merkel da ministar kula da al'amuran iyali da aka haifa a yankin gabashin Jamus din cikin ministoci 16 na gwamnatin Merkel na zaman tamkar wani yanki mara shinge ga gabashin Jamus. Za a iya bayyana hakan da wata alama ta hadin kan Jamus. Tun bayan sake hadewar Jamus, lokaci na ta tafiya kuma har kawo yanzu masu fada a ji na yammacin Jamus na ci gaba da mamaye dukkanin mukamai. Har yanzu akwai karancin wakilcin masu fada a ji daga gabashin Jamus a kamfanoni da jami'o'i da kafafen sadarwa, abin takaici har da Deutsche Welle. Har sai an shawo kan wannan matsalar sannan za a magance bambancin da ke tsakanin gabashi da yammacin Jamus, sannan a kai ga cimma hadin kai na bai daya a kasar baki daya.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani