Sharhi: Rashin nasarar ziyarar Kofi Annan a Damascus
March 12, 2012A duk lokacin da wani sanannen mutum, musamman wanda ya taba samun lambar zaman lafiya ta Nobel ya shiga neman sulhu a wani yanki dake fama da rikici, akan dora fata mai yawa game da samun nasarar kokarin sa. A wannan karo ma haka abin yake, lokacin da Kofi Annan, tsohon dan diplomasiya da majalisar dinkin duniya da kungiyar hadin kan Larabawa suka nada shi a matsayin wakilin su na musmaman zuwa Damascus domin neman sulhu a rikicin Syria. A can din an danka masa nauyin jan hankalin shugaba Bashar al-Assad da yan adawan kasar su ajiye makaman su. To sai dai Assad ya tsaya kai da fata game da ci gaba da wannan yaki.
Kamar yadda shugaban na Syria ya sha fadi tun daga makonnin baya, bai kamata a sasauatawa wadanda ya kira yan tarzoma ba, kamar yadda yake kiran masu kkarin tabatar da juyin juya hali a kasar ta Syria. A bisa duban farko, za'a ga kamar kokarin da Kofi Annan yayi bai sami nasara ba, domin kuwa a maimakon dan mukin kama karyan na Syria ya amince da yarjejeniyar tsagaita bude wuta, sai ma ya tura karin sojoji da suka bude wuta kan yan zanga-zanga a lardin Idlib, dandalin masu neman juyin juya halin a yammacin Syria. To sai dai tun da farko aka san cewar kokarin neman sulhun na Kofi Annan ba zai zama abu mai sauki ba, saboda tun daga watannin baya, shugaba Bashar al-Assad ya nunar da kansa a matsayin mutumin da baya jin shawara, kuma baya koyon darasi.
Aikin jami'in sulhu na kasa da kasa kamar Kofi Annan shine ya nunawa mutum kamar Bashar al-Assad cewar lokacin sa da lokacin gwamnatin sa ya kare ta fuskar siyasa. Ana iya ganin hakan a fili a game da Syria, ko da shike watakila za'a dan dauki loakci kafin kayar da mulkin na Assad a zahiri. Idan har ana ci gaba da samun karin sojoji dake kauracewa sansanin sa, Rasha kuma ta canza ra'ayin ta a game da Assad, kuma Syria ta kara shiga matsalar tattalin arziki, gwamnatin dake mulki zata gane cewar lokacin ta ya kare babu gudu, babu ja da baya a zanga-zangar da aka fara yanzu shekara guda.
To sai dai kuma ko da shike bisa manufa, mulkin Bashar al-Assad ya kare a Syria, amma dan mulkin kama karyar yana ci gaba da amfani da karfin makamai kan al'ummar sa. Yana sane da cewar Amerika da kawayen ta kasashen yamma suna kyamar kaiwa kasar sa hari, sabopda tsoron yin hakan zai jefa yankin gabas ta tsakiya baki daya cikin hali na rudami. Yana sane da cewar yiwuwar harin Israila kan kasar Iran zai tilastawa shugaba Barak Obama ya goyi bayan kasar ta Yahudawa, yadda bashi da sauran wata kafa ta tayar da wani yakin dabam a Syria. Musamman kuma, yana sane da cewar tashin rikici a gabas ta tsakiya, zai haddasa farashin man fetur yayi tashin gwauron zabo a kasuwnanin duniya. Assad saboda haka yake sa ran cewar kasashen yamma basa iya yi masa komai, yayin da Rasha zata ci gaba da bin manufofin sa na hana kasashen na yamma suyi masa komai.
Shima a lokacin ziyarar sa a Damascus, Kofi Annan ya baiyana adawa da neman sulhunta rikicin na Syria ta amfanida karfin soja. Ira ma kungiyar hadin kan Larabawa a lokacin ganawar da tayi a karshen mako, ta daidaita a gameda bukatar sjhawo kan rikicin ta hanyar shawarwari. Ziyarar ta Annan ba za'a ce bata sami nasara ba, saboda a sakamakon ta, akalla Assad ya amince da bude wata kafa da kungiyoyin agaji suke amfani da ita domin taimakon wadada suka tagaiyara a rikicin na Syria. Wannan kuwa wata babbar nasara ce da ta samu sakamakon ziyarar ta Kofi Annan da ganawar sa da Bashar al-Assad.
Mawallahi: Scheschkewitz/Aliyu
Edita: Zainab Mohammed