Sharhi: Turkiya a rikici da Siriya
October 5, 2012Take-taken shugaban Siriya Basahr al-Assad bai bambamta da na shugabannin ƙasashen Larabawa da aka hamɓarar da su a baya bayan nan ba. Yaƙin da yake yi da 'yan adawa na ƙara yi muni. Kuma harin gurnati da Siriya ta kai kan wani ƙauyen ƙasar Turkiya da ya halaka mutanen da ba su san hawa ba su san sauka ba, wani yunƙuri ne da Assad yayi na tsokanar maƙwabciyarsa da ta fi shi ƙarfi. Shugaba Bashar al-Asad dai na son ya bar baya da ƙura a wannan yanki, idan ya bar mulki.
Turkiya kuwa ta mayar da martani da ya dace wato na soji ba tare da mamaye yankin ƙasar Siriya ba. Bai kamata firaministan Turkiya Recep Tayyip Erdogan dake samun goyon bayan ƙasashen duniya ya ɗauki wani ƙarin matakan soji na raɗin kai a kan Siriya ba. Bai kamata kuma amincewar da majalisar dokokin Turkiya ta yi na ɗaukar matakan soji kan maƙotanta da suka tsokane ta zama wata dama ga ƙasar dake zama memba a ƙungiyar tsaron NATO, ta ɗauki matakan gaban kai ba ko ta bari ƙawancen ƙasa da ƙasa da ƙawayenta na Turai su ƙarasa mata yaƙin ba. Saƙon da al'ummar Turkiya suka bayar na adawa da shiga yaƙi da Siriya bayan ƙudurin majalisar dokokin a bayyane yake kuma ya nuna a fili cewa dole Erdogan yayi takatsantsan a siyasar cikin gida.
Dole Turkiya ta yi sara tana duban bakin gatari. Bisa la'akari da halin da ake ciki ana iya cewa kalaman da ministan harkokin wajen Turkiya Ahmet Davutoglu yayi cewa ƙasarsa ba ta da matsala da dukkan maƙwabtanta sun ruguje. Hasali Turkiya na da matsala da da maƙwabtanta. Goyon bayan da take samu daga ƙasashen yamma ya taƙaita ne a kan rikicin Siriya, kuma zai kau idan ga misali ta samu matsala da ƙasashen Armeniya, Girika ko Bulgariya.
Ba a san kuma irin martanin da Iran da kuma Rasha za su mayar ba. Har yanzu fadar Kremlin na goyon bayan Assad. Sai dai shugaban Rasha Vladimir Putin dole yayi tunani mai zurfi ko ya ci-gaba da marawa wani ɗan mulkin kama karya da ya kusa faɗuwa ko kuma ya jefa wata babbar ƙawarsa a yankin cikin halin rashin sanin tabbas. Idan ana batun Turkiya ne to Iran za ta taƙaita kakkausar sukar da take wa Ankara a baka, ba za ta taɓa gwajin ƙarfin sojinta a kan Turiya ba.
Ko da yake Rasha da Iran ka iya jan kunnen Turkiya, idan ta ƙasar ta bijire. Rasha ka iya daina sayar ma Turkiya iskar gas yanzu da ake dab da shiga lokacin sanyin hunturu. Ita kuma Iran ka iya janye wasu albarkatun ƙasar domin taka wa Turkiya biriki a bunƙasar tattalin arzikin da take samu, abin da zai durƙusar da ƙasar.
Hakan kuwa ba zai yiwa tarayyar Turai ko Amirka ko NATO dadi ba. Saboda haka shawara ga Erdogan ita ce ya yi watsi da ɗaukar matakan raɗin kai a kan Siriya, ya nemi goyon bayan ƙasashen yamma da kuma Majalisar Ɗinkin Duniya. Matakan ramuwa da taimaka wa 'yan adawar Siriya sun wadata ka da ya bari Turkiya ta zama musabbabin gwabza wani yaƙi a yankin.
Mawallafa: Baha Güngör / Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu