1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Sharhi: Turkiyya bayan yunkurin juyin mulki

Banu Güven LMJ/RGB
July 15, 2021

Shekaru biyar bayan yunkurin juyin mulki da kuma matakin da yake dauka na kokarin hana 'yan adawa katabus, har yanzu Shugaba Erdogan na fargabar rasa karfin ikonsa.

Weltspiegel 19.05.2021 | Türkei Ankara | Recep Tayyip Erdogan, Präsident
Shugaba Recep Tayyip ErdoganHoto: Murat Cetinmuhurdar/PPO via REUTERS

Banu Güven ta fara sharhin da cewa: Shekaru biyar ke nan bayan da Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya sha da kyar daga yunkurin juyin mulkin da aka yi masa, a ranar 15 ga watan Yulin 2016. Juyin mulkin kuma da ya zargi tsohon abokinsa Shehin Malami Fethullah Gulen da ke zaman neman mafaka a Amirka. A karkashin dokar ta baci ta tsawon shekaru biyu, Erdogan ya yi amfani da duk damar da yake da ita wajen kawar da duk wani abu da ka iya zama tarnaki gare shi wajen ci gaba da mulki. Sai dai a yanzu Erdogan na cike da fargabar rasa mulki fiye da kowane lokaci. Karin Bayani:  Turkiya: Hana ayyukan Hizmet ta Gülen
Sakamakon kuri'ar jin ra'ayin jama'a da aka gudanar a baya-bayan nan, na nuni da cewa, da za a gudanar da zaben shugaban kasa a yanzu zai yi wuya a zabe shi. Cikin dalilan da suka janyo raguwar magoya bayansa, har da kura-kuren da yake ta yi tsawon shekaru biyar din da suka gabata, kura-kurai irin wadanda masu mulkin danniya ke aikatawa.

An kama daruruwa bisa zargin alaka da GulenHoto: picture-alliance/AP Photo/O. Duzgun

Bayan yunkurin yi masa juyin mulkin da bai yi nasara ba da kafa dokar ta baci, Erdogan ya fara mulkin danniya da ba a taba ganin irinsa ba a tarihin siyasar kasar. Ya kori dubban mutane daga aiki, kama daga jami'an sojoji da alkalai da masu shigar da kara da malaman makaranta ba tare da wani dalili ba, tare da maye gurbinsu da 'ya'yan jam'iyyarsa da ke mara masa baya wadanda kuma ba su da kwarewa. Karin Bayani:  An dakile yunkurin juyin mulkin Turkiyya
Ya auna'yan  jarida da marubuta da kuma mambobin kungiyoyin farar hula zuwa gidan kaso, ba tare da wani fata na sakinsu ba. Dama tuni 'yan siyasa da suka hadar da masu adawa da shi suka sha dauri. A tsawon wadannan shekaru biyar, Erdogan na kira duk wani wanda ya kalubalance shi da dan ta'adda ko kuma dan leken asirin kasashen ketare. Azabtarwa da musgunawa a hannun 'yan sanda sun zama ruwan dare. Ya ma yi amfani da dokar ta bacin  wajen rufe duk wasu kafafen yada labarai ko kuma shafukan daidaikun mutane da ke sukan salon mulkinsa. Zai wahala a iya kau da idanu a kan wannan mugunta, ko da kuwa daga ma su tausayawa Erdogan ne. Karin Bayani:  Turkiya: An kama wasu lauyoyi
Erdogan Ya saka dogon buri kan karfin fada a ji a tsarin shugabanci na kasa da kasa, abin da ya biyo baya kuwa, ya shafi baki dayan 'yan Turkiya. Ko mai yake tunani yayin da ya aike da babban limamin cocin nan dan kasar Amirka Andrew Brunson zuwa gidan kaso da kuma zarginsa da alaka da Kungiyar Gulen? Erdogan ya bukaci tsohon shugaban kasar Amirka Donald Trump ya mayar da Fethullah Gulen da ke neman mafaka a Amirkan zuwa gida, kafin ya saki limamin Cocin. A maimakon abin da ya bukata, Turkiya ta fuskanci takunkuman karya tattalin arziki da sauyi ta fuskacin kasuwanci. Kudin Lira na kasar ya karye da kaso 40 cikin 100 idan aka kwatanta da dalar Amirka cikin kwanaki kalilan.

Al'ummar Turkiyya a lokacin bikin ranar samun 'yanciHoto: picture-alliance /H. Altunoz
Banu Güven Hoto: Privat

Erdogan na zabar abokansa da 'yan uwansa wadanda za su yi masa biyayya ido rufe. Saboda haka, babu mai fada masa idan ya yi kuskure. Wadanda ya zagaye kansa da su, sun kafa hanyoyin azurta kansu. Wani tsohon shugaban 'yan mafiya ya bayyana yadda ake gudanar da wasu nau'ikan kasuwanci abin zargi a gwamnatin Erdogan ciki har da firgita manyan 'yan kasuwa da cewa za a alakanta su da 'yan kungiyar Gulen. Erdogan ya maye gurbin daraktocin babban bankin kasar cikin shekaru biyu, saboda ba su aminci da tsare-tsarensa na lamuni ba. Duk da tattalin arzikin  ya kunyata shi, Erdogan ya dage kan cewa saka riba mai yawa ne ke janyo matsalar hauhawar farashi. 
Nada sirikinsa Berat Albayrak matsayin ministan kudi ba mataki ne mai kyau ba. A karshe Albayrak ya yi ritaya bayan ya gaza tabuka komai kan maido da darajar kudin kasar, matakin da masu hada-hadar kudi suka yi maraba da shi. Sai dai lokaci ya kure, ba za a iya farfado da Lirar ba. Tamkar duk masu mulkin danniya, Erdogan ba ya maraba da batun bai kowa dama. Ya taba bayyana yunkurin yi masa juyin mulkin da bai yi nasara ba da wata kyauta daga Alllah. Yana gode masa da ya ba shi damar yin iko da kasar baki daya. Wani karin kuskure na masu mulkin danniya. A yanzu dai tamkar shugaban kasar ya kai wani geji da ba zai iya koma wa baya ba, a salon mulkin na danniya.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani

Nuna karin labarai