Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da Shugaba Mahamadou Issoufou na Nijar dukkansu biyu suna sha'awar a gansu tare a bainar jama'a. Kuma ziyarar ta shugaban na Nijar a Jamus ita ce ziyararsa ta uku a Berlin tun daga shekara ta 2013. A manyan taruka na kasa da kasa ma kamar na bara na kungiyar G20 da kasashen Afirka, Shugaba Issoufou ya kasance bakon da aka yi maraba da shi a Berlin. Ita ma Merkel ta kai masa ziyara birnin Yamai a 2016, inda ta yi masa alkawarin karin taimakon raya kasa na miliyoyin Euro gami da na kayan aikin soji. Tun sannan an bude wata makaranta da ake kira makarantar Angela Merkel.
Nijar kawa ga kasashen Turai
Nijar daya a cikin kasashe mafi talauci a duniya, babbar kawa ce ga gwamnati a Berlin da Tarayyar Turai mai shelkwata a birnin Brussels. A yankin Sahel, kasar tana makwabtaka da kasashen Mali da Libiya da ke fama da rikicin 'yan bindiga, a kudu da ita mayakan Boko Haram daga Najeriya ne ke ketare kan iyakokinta, yayin da a gabas kasar Chadi ce da ke karkashin mulkin kama karya na Shugaba Idriss Deby.
Saboda haka nahiyar Turai tana farin ciki da zuwa yanzu Nijar din ta kare kanta daga shigar da ita cikin rikice-rikice na yankin. Hakazalika Turai na jin dadin yadda gwamnati a Yamai ta rufe hanyoyin da 'yan ci-rani ke bi don kai wa arewacin kasar. A kan iyakokinta da Mali da Najeriya sojojinta na yaki da 'yan tarzoma daga kasashen biyu.
Saboda haka shugabar gwamnati Merkel na da kwararan dalilai na mika godiya ga Shugaba Issoufou. Za ta iya amfani da ganawarsu ta nunawa Jamusawa cewa tana samun nasara a aikin dakile kwararar bakin haure. A daura da haka, kyakkyawar dangantaka da Berlin, za ta ba wa Shugaba Issoufou damar rage yawan dogaro da tsohuwar 'yar mulkin mallaka wato Faransa. Ana iya cewa Issoufou ya samu sabuwar kafar samun kudin shiga ga Nijar.
Merkel da Issoufou na bukatar juna
Watakila ana iya cewa gwamnatocin biyu na cin amfani juna. Amma a fakaice ba haka lamarin yake ba. Misali ga 'yan ci-rani da yanzu ke bi ta barauniyar hanya a cikin Hamada, daruruwansu ke mutuwa ba tare da an sani ba. Akwai masu sukar sa cikin gida da cewa ya zama dan amshin Shatar kasashen ketare. Yawan taimako da ya samu daga Berlin da Brussels na kara yawan sukar da yake sha. Wanda kuma bai yi hattara ba sai a jefa shi kurkuku ko ya yi hijira, kamar yadda ya faru ga daya daga cikin manyan 'yan adawa Hama Amadou a zaben 2016. A farkon wannan shekara ta 2018 gwamnati ta tsare manyan shugabannin kungiyoyin farar hula tsawon watanni a kurkuku, saboda shirya zanga-zangar adawa da sabuwar dokar kasafin kudin kasa.
'Yancin 'yan jarida da a baya Nijar ta sha yabo saboda mutunta shi, yanzu an samu sauyi, inda jami'an tsaro ko hukumomin shari'a ke farautar daidaikun 'yan jarida. Babban misali shi ne yadda aka kori dan jaridar nan Baba Alpha zuwa Mali bayan an zarge shi da mallakar takardun zama dan kasar Nijar ba bisa ka'ida ba.
Ya kamata Merkel ta fito fili ta fadawa takwaranta na Nijar cewa muradun Jamus a yankin Sahel ba sa nufin a yi fatali da tsarin demukuradiyya da 'yancin dan Adam. Dole ne Shugaba Issoufou ya saurari masu sukar lamirinsa da kunnen basira, ya kuma yi hattara da masu ra'ayin rikau a cikin gwamnatinsa, ya kuma fito fili ya fadawa 'yan Nijar cewa burinsa ba shi ne ci gaba da mulki ta kowane hali ba.