1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhin Jaridun Jamus a kan Afirka

Mouhamadou Awal Balarabe
June 14, 2024

Shugaba Lazarus Chakwera na Malawi ya soke tafiyar da ya shirya zuwa Bahamas domin nuna alhini dangane da rasuwar mataimakinsa Saulos Chilima wanda ya rasu a hadarin jirgin sama

Wasu daga cikin Jaridun Jamus
Wasu daga cikin Jaridun JamusHoto: Jens Kalaene/dpa/picture alliance

Za mu yaye kallabin shirin da sharhin ZEIT ONLINE mai taken: "Jirgin soja da ke dauke da mataimakin shugaban kasar Malawi ya yi batar dabo", inda ta ce  Saulos Chilima da sauran jami'an da ke cikin sun riga mu gidan gaskiya bayan bacewar jirginsu sakamakon hatsari. Sai dai  Shugaba Lazarus Chakwera ya soke tafiyar da ya shirya zuwa Bahamas, inda a cikin jawabinsa ya ce hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Malawi ta bukaci matukin jirgin da ke dauke da mataimakin shugaban kasar da ya koma da baya saboda mummunan yanayi a sararin samaniya kafin a daina jin duriyar jirgin.

Marigayi mataimakin shugaban kasar Malawi Saulos Chilima Hoto: Eldson Chagara/REUTERS TV

Chilima ya kasance mataimakin shugaban kasar Malawi tun 2020. Amma jaridar ZEIT ONLINE ta ce yana fuskantar bincike kan zargin almundahana da karbar na goro.  An ma taba kama shi a karshen 2022 duk da cewar a watan Mayu, masu gabatar da kara sun yi watsi da tuhumar ba zato ba tsammani. Saulos Chilima ya kasance shugaba na biyu da ya rasa ransa a hadarin jirgi a cikin wata guda baya ga shugaban kasar Iran Ibrahim Raissi.

Yanzu kuma sai fannin siyasa, inda die tageszeitung ta yi tsokaci kan abin da ta kira: "Kwanaki na rashin tabbas a Afirka ta Kudu", jaridar ta ce a daidai lokacin da aka kafa sabuwar majalisar dokoki a wannan Juma'a ba tare da jam'iyyar ANC ta samu rinjaye ba, an bude babin kafa gwamnati mai zuwa cikin halin rashin tabbas. Jaridar ta ce makonni biyu bayan da 'yan Afirka ta Kudu suka yi  jerin gwano a gaban rumfunan zabe cikin sanyi, har yanzu ba su da masaniya game da yadda sabuwar gwamntin za ta kasance.

Jacob ZumaHoto: AP/picture alliance

die tageszeitung ta ce akwai rashin tabbas game da rantsar da majalisar da zaben shugabanninta saboda sabuwar jam'iyyar MK da tsohon shugaba Jacob Zuma ya kafa ta sha alwashin kawo nakasu. Bisa ga kundin tsarin mulkin Afirka ta Kudu dai, akalla kashi daya cikin uku na 'yan majalisa ne ya kamata su hallara kafin a bude zaman majalisa. Ko da shi ke ba zai zama wata matsala ga ANC ta samun wannan adadi ba, amma kaurace wa zaman da Jam'iyyar MK ke yi na nuna irin kalubale da ke gaban jam'iyyar ANC da ke mulki.

A game da halin yaki da ake ciki a yakin basasar Sudan kuwa, sharhin die tageszeitung ya ce "Asibiti ya zama wurin kai farmakin yaki ". Jaridar ta ce asibitin karshe da ke gudanar da harkar jinya a garin El Fasher na yankin Darfur ya samu kansa cikin wani mummunan yanayi bayan da dakarun RSF suka kutsa tare da lalata shi a yunkurinsu na neman madafun iko. Saboda haka ne kungiyar agaji ta kasa da kasa Doctors Without Borders ko Médecins Sans Frontières (MSF) tare da hadin gwiwar hukumomin lafiya na Sudan suka rufe asibitin bayan da 'yan bindigar suka lalata ofisoshi tare da sace kudaden albashi da abinci da magani da kuma motoci.

Garin al-Fasher na yankin DarfurHoto: AFP

die tageszeitung ta kara da cewar El Fasher ya zama wani fagen daga saboda shi ne babban birni daya tilo daga larduna biyar na yankin Darfur da har yanzu ba ya karkashin ikon RSF. Amma kuma wannan ba shi ne karon farko da ake irin wannan ta'asa a yankin ba. Sai dai a wannan karon tun watan Mayu ne dakarun RSF ke kai hare-hare kan mai uwa da wabi kan cibiyoyin soji da kuma farar hula hari a El Fasher, lamarin da ya sa dubban mutane kaurace wa matsugunansu.

Ita kuwa jaridar Neue Zürcher Zeitung ta mayar da hankali kan hakkin mata a karkashin sharhinta mai taken: "Gambiya na son zama kasa ta farko a duniya da ta za ta halarta kaciyar mata." Jaridar ta ce 'yan mata miliyan 230 a duk duniya ne aka yi wa kaciya, amma masu fafutuka na fargabar cewar wasu kasashe za su iya koyi da karamar kasar ta yammacin Afrika wajen farfado da yi wa mata shayi.

Neue Zürcher Zeitung ta ce bisa kididdigar da Asusun Kula da Kananan Yara ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ta nunar da cewar yawancin 'yan mata miliyan 144 da kaciyar ta  shafa na da zama ne a kasashen Afirka yayin da sama da miliyan 80  ke rayuwa a nahiyar Asiya. Jaridar ta jadadda cewar an fi yin kaciyar ce a kasashen da ke da rinjayen Musulmi da wadanda ke bin addinin gargajiya. kuma kasar da ta yi kaurin suna a duniya a fannin kaciyar mata ita ce Somaliya inda aka yi wa kashi 99% shayi, yayin da Gambiya ke biya mata baya da kashi uku cikin hudu na 'yan matan kasar.