Sharhin Jaridun Jamus a kan Afirka
October 10, 2025
die tageszeitung: Babu fata a Las Vegas, Kamaru
Jaridar ta ce: A lokutan damuna a wannan yanki na Las Vegas na Kamaru ana fama da ambaliyar ruwa, yanki na hudu a babban birnin kasuwancin kasar Kamaru wato Douala, ya yi hannun riga da takwaransa na Amurka. Wannan yanki na dauke da bukkoki a matsayin gidaje, ruwa na kai wa iya gwiwa. Tun a shekara ta 2016 al'ummar yankin da ke magana da harshen Turancin Ingilishi suka shiga tsaka mai wuya, bayan da fada ya barke tsakanin sojojin gwamnati da 'yan aware masu ikirarin ballewa tare da kafa kasar Ambazoniya.
Kungiyar Kare Hakkin dan Adam da Human Rights Watch ta ruwaito cewa: Rikicin ya halaka mutane 6000 tare da tilasta dubbai barin gidajensu. A zaben ranar 12 ga watan Oktoba na 2025, akwai hasashe mai karfin gaske da ke nuna yiwuwar sake zabar shugaban kasar mai ci Paul Biya . Mai shekaru 92, Biya ya kasance shugaban kasa mai ci mafi tsufa a duniya. Tun a shekara ta 1982 yake shugabanci a Kamru, a yanzu yana neman wani wa'adin mulki na tsawon shekaru bakwai.
Ita kuwa jaridar Die Zeit ta rubuta sharhinta ne mai taken: "Har yanzu ina da ragowar kwayoyin magani biyu" Yanayin lafiya tun bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya rage tallafin raya kasashe, wasu likitoci a Yuganda na yin wankin mota domin samun kudin kula da marasa lafiyar da suke da su. Sai dai wasu a kasar, na ganin Trump din abin alfahari ne.
Jaridar ta ce: Ga misali kwanaki biyu bayan da Trump ya ayyana dakatar da agajin raya kasa da Amurka ke bayarwa, 'yar kasar Yuganda Jennifer Okello (da ba sunanta na gaskiya ba ke nan saboda ba ta son a bayyana sunanta na ainihi) ta yanke shawara gara ta mutu. Matar da mijinta ya rasu ya bar ta da yara biyar, na dauke da kwayar cutar HIV AIDs mai karya garkuwar jiki. Tilas ne Okello ta sha magani har karshen rayuwarta, sai dai matakin na Trump ya karya mata gwiwa. Hakan ya sa ta daina cin abinci da shan maganin nata, domin tana fargabar in ya kare ba za ta samu wani ba.
Ba mu karkare da jaridar Neue Zürcher Zeitung a sharhinta mai taken: "Sarkin ba zai iya kauce wa sauyi ba, matasa na zanga-zanga a Moroko." Jaridar ta ce: Mutane da dama da ke shirin tafiya hutu ko yawon bude idanu a kasar da ke arewacin Afirka, na kara nazari a 'yan kwanakin nan. Shin za su iya tafiya zuwa Casablanca ko Marrakesch kuwa, a daidai lokacin da matasa ke zanga-zangar neman sauyi a biranen kasar da dama?
Kimanin makonni biyu ke nan matasan Moroko ke zanga-zanga a fadin kasar, domin neman a yi gyara a fannin ilimi da kiwon lafiya da kuma nuna adawa da cin-hanci da rashawa. Duk da cewa sun ce zanga-zangar ta lumana ce, ana samun tashe-tashen hankula a 'yan kwanakin nan. Ma'aikatar cikin gida ta kasar ta ruwaito cewa, kimanin masu zanga-zanga uku ne 'yan sanda suka harba.
Zanga-zangar ka iya yin kamari, a daidai lokacin da kasar ke kara dogaro a kan yawon bude idanu. A shekara ta 2024, Moroko ta kasance kan gaba a kasashen da ake zuwa yawon bude idanu a Afirka da baki miliyan 17. Wannan ya sanya ta yi wa kasar Masar fintinkau a bara, kana ana sa ran adadin ya karu zuwa mutane miliyan 26 a shekara.