Sharhin Jaridun Jamus akan nahiyar Afirka
November 21, 2025
Ba mu fara da jaridar Neue Zürcher Zeitung a sharhinta mai taken: Miliyan 100 domin layin dogo, miliyan 50 ga Sudan. Gwamnatin tarayya a Switzerland na son amfani da miliyoyin kudin haraji daga yankin canton na Geneva nan take.
Jaridar ta bayyana cewa halin jin-kai a Sudan ya kai wani wadi na tsaka mai wuya, tamkar takaita ta'azzarar lamarin ne.
Labaran da ke fitowa, na da tayar da hankula. Kungiyoyin bayar da agaji da jami'an diplomasiyya, sun bayyana cewa halin da kasar da ke yankin Arewa maso Gabashin Afirka ke ciki na kamanceceniya da na kowanne yanki da ke fama da yaki.
Sama da mutane miliyan 12 ne suka tarwatse sakamakon yaki, sai dai hankulan Kasashen Yamma da ma agajin jin-kan da suke bayarwa, bai kai na sauran yankunan da ake yaki ba.
A yanzu gwamnatin tarayya, na son daukar wani mataki a madadin Switzerland ta hanyar amincewa da karin bashin Frank miliyan 50 cikin gaggawa. Za a yi amfani da kudin, wajen kai kayan agajin jin-kai da al'ummar Sudan da ke cikin kangin yaki da yunwa ke bukata nan take.
Suna son tsarin Shari'ar Musulunci, in ji jaridar Die Zeit cikin sharhinta mai taken: A Mali, masu ikirarin jihadi na hana kai kayan masarufi zuwa babban birnin kasar. Ko ana shirin samar da sabuwar kasar Musulumci a yankin Afirka ta Yamma?
Jaridar ta ce: Al'ummar Mali, sun saba da ganin yadda masu ikirarin jihadi ke bankawa tankokin dakon kaya da ke dauke da kayan masarufi wuta. 'Yan kungiyar JNIM da ke ikirarin taimakon Musulunci da Musulmi, ke aikata hakan.
Sai dai kungiya ce da ke da alaka da kungiyar 'yan ta'addan al-Qa'ida, kuma sannu a hankali suna kokarin cimma burinsu na kafa kasar Musulunci. Wannan ita ce fargabar masu sanya idanu, sakamakon yadda suke kai hare-hare kan tankokin dakon kaya.
Kungiyar JNIM ta yi nasarar yin safarar ruwa da musamman man fetur daga kasashen Senegal da Côte d'Ivoire, zuwa Bamako babban birnin kasar. Suna kokarin tsayar da birnin, wanda ke da yawan al'umma miliyan uku cik.
Za mu karkare da jaridar die tageszeitung a sharhinta mai taken: Abun na dangi ne, shugabar kasar Tanzaniya Samia Suluhu Hassan ta nada danginta masu yawa ministoci. Haka abin yake tun da jimawa, a wasu kasashen Afirka da dama.
Jaridar ta ce: Bayan gagarumar zanga-zangar da ta biyo bayan zaben da aka gudanar a watan Oktoba, Shugaba Samia Suluhu Hassan ta nada ministcoi 27 da mataimakansu 29 a fadarta da ke Dodoma babban birnin kasar Tanzaniya.
A sabuwar majalisar zartaswarta, akwai tarin matasa masu jini a jika. Sai dai rahotanni sun nunar da cewa, suna da alaka da Shugaba Samia ko kuma Jakaya Kikwete da ya kasance tsohon shugaban kasar kana tsohon shugaban jam'iyyar CCM da a yanzu Samia ke jagoranta.
'Yan adawa sun fuskanci wariya kafin zaben, an yi ta kama su tare da tuhumarsu da laifin cin amanar kasa. Hukumar Zaben kasar ta ce Samia ta samu nasara da kaso 98 cikin 100, a zaben da tun a ranar da aka gudanar da shi zanga-zanga ta barke a fadin kasar. Zanga-zangar da jami'an tsaro, suka murkushe da karfin tuwo.
Kungiyoyin Kare Hakkin dan Adam, sun nunar da cewa an kashe kimanin masu zanga-zanga 1000. A makon da ya gabata, shugaban hukumar kare hakkin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya Volker Türk ya bukaci Shugaba Samia ta gaggauta gudanar da bincike tare da hukunta wadanda ke da hannu a kisan.