1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhin Jaridun Jamus akan nahiyar Afirka

Zainab Mohammed Abubakar
January 30, 2026

Sojojin Yuganda sun kai samame gidan jagoran adawa Robert Kyagulanyi da aka fi sani da Bobi Wine tare da yin awon gaba da mai dakinsa Barbara Kyagulanyi

Jagoran adawa na kasar Yuganda Bobi Wine tare da matarsa Stimmabgabe
Jagoran adawa na kasar Yuganda Bobi Wine tare da matarsa Stimmabgabe Hoto: Thomas Mukoya/REUTERS

Jaridar die tageszeitung ta ce Barbara Kyagulanyi ta tsaya a gaban sojojin sanye da rigar barci, kamar yadda ta shaidar a yayin da take bayanin yanayin da suka sameta da kuma yadda jami'an suka yi ci zarafinta a kokarin samun bayanin inda mijinta yake.

Barbara ta ce sojojin sun shake makogwarona, suka daga ni sama suka yi kokarin tilasta mini in bayyana kalmar sirri ta bude wayar salulata. Amma Barbara Kyagulanyi, wacce aka fi sani da "Barbie," ba ta bayyana kalmar sirrin ba. Wannan turjiya da nuna ya sa sojojin suka yi mata lahani da cin zarafin da ya kai ta kwanciya a asibiti. Duk da cewa sojoji suna tsaye a wajen kofar dakinta da take jinya, 'yan jarida sun sami damar ziyartarta.

Wasu daga cikin Jaridun JamusHoto: Jan Woitas/dpa/picture alliance

Sojojin Yuganda a halin yanzu suna neman mijinta Bobi Wine a duk fadin kasar. Shahararren mawaki kuma jagoran 'yan adawa ya fafata da shugaban kasar Yoweri Museveni mai dogon zamani a zaben tsakiyar watan Janairu, wanda ya yi nasara da kashi 72 cikin 100 na kuri'un da aka kada. Wine ya bayyana cewa an yi magudi tare da kira da a yi zanga-zanga. Hakan ba zai rasa nasaba da ziyarar da jami'an tsaro suka kai gidansa ba, ba su same shi ba amma sun tarar da matarsa ​​kawai. Wine ya sami nasarar tserewa cikin lokaci.

Ita kuwa jaridar Welt online sharhi ta yi game da makudan kudade da Najeriya za ta kashe wajen neman tallafin yaki da 'yan bindigar jeji a yankin arewacin Najeriya.

Shugaban Amurka Donald Trump Hoto: Denis Balibouse/REUTERS

Shugaban Amurka dai yayi gargadi dangane da kai hari kan kiristocin arewacin Najeriya, duk da cewar harin na kan mai uwa da wabi ne maharan ke kaiwa kan al'ummomin yankunan musamman a kauyuka. Tuni dai Donald Trump ya ayyana daukar mataki na kai dauki a kan aika aikan masu tsattsauran ra'ayin. 

Gwamnatin Abujar dai  za ta kashe dala miliyan tara don wanke kanta a siyasance kan zargin na Washinton, ta amfani da wani kamfanin kamun kafa da zai taimaka wanke Najeriyar daga zargin da mahukunta na Amurkan ke yi. An dora wa kamfanin na kwararru a fannin kamun kafa alhakin karyata zarge-zargen tsananta wa Kiristoci, bugu da kari wanke hukumomin tsaron kasar da tuni aka shafa wa kashin kaji.

Abin da ya sake janyo hankalin Amurkan a kan Najeriya dai, shi ne lamarin da ya auku a jihar Kaduna, inda wakilan coci da mazauna kauyen Kurmin Wali suka ce, wasu mutane dauke da makamai sun kai hari kan majami'u da dama a yayin ibada kuma sun sace sama da masu ibada 160.

Wasu yan gudun hjirar Sudan ta KuduHoto: Ashraf Shazly/AFP

"Kada ku bar kowa da rai!" Wannan shi ne taken labarin da jaridar Süddeutsche Zeitung ta wallafa a kan barazanar sabon yaki da ke neman barkewa a Sudan ta Kudu. Jaridar ta ce, Shugaba Salva Kiir da mataimakinsa da aka hambarar Riek Machar suna sake tattara sojojinsu domin yakar juna. Tuni dai mutane suka fara tserewa daga babban birnin Juba.

A yayin da ya ke jawabi mataimakin shugaban rundunar sojin Sudan ta Kudu, Janar Johnson Olony, ya umurci sojojin kada su bar kowa da rai kama daga tsofaffi zuwa yara, har ma da kaji, nan take sojojinsa suka yi ihu da tafi, kafin su bi umurnin tafiya yaki a jihar Jonglei da ke kudancin kasar, yankin da a cewarsa shi ne tushen matsalolinsu.

Alamu suna nuna sake barkewar yaki a Sudan ta Kudu. Jaririyar kasa, kuma inda ba a taba samun zaman lafiya ba tun bayan samun 'yancin kai a 2011 saboda yakin madafan iko.
 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani