1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhin Jaridun Jamus kan Afirka

Mohammad Nasiru Awal
December 18, 2020

Sace daruruwan daliban makarantar sakandare a garin Kankara da ke a jihar Katsinar Najeriya ya dauki hankalin jaridun Jamus a labarai da sharhuna da suka rubuta a wannan mako kan nahiyar Afirka.

Symbolbild Pressespiegel
Hoto: Jan Woitas/dpa/picture alliance

Jaridar Süddeutsche Zeitung ta yi tsokaci tsokaci kan 'yan bindiga dauke da manyan makamai da suka yi awon gaba da dalibai fiye da 340 lokacin da suka yi dirar mikiyya a kan makarantar sakandare ta garin Kankara da ke jihar Katsina a Arewa maso yammacin Najeriya. Ko da yake rahotanni daga mahukuntan yankin na cewa an ceto yaran daga hannun 'yan bindigar, amma jaridar ta ce wannan lamari ya yi tuni da garkuwar da aka yi wa 'yan mata 'yan makarantar Chibok su 276 a 2014 lokacin da Boko Haram ta kai hari a makarantarsu da ke Arewa masu gabashin Najeriya.

Makantar Sakandaren Kankara a jihar KatsinaHoto: Abdullahi Inuwa/REUTERS

Yankin arewacin Najeriya dai na fama da matsalar ayyukan 'yan tarzoma da masu garkuwa da sace mutane don neman kudin fansa. Ko da yake a kullum mahukunta na ikirarin daukar sahihan matakan kawo karshen wannan masifa, amma har wayau ba a gani a kasa ba. Fata dai shi ne a wannan karo gwamnatin Najeriya za ta ba wa abin muhimmancin da ya kamata don ceto yankin daga wadannan bata gari.

 Mayar da hannun agogo baya.

'Yan makarantar sakandaren Kankara da aka sakoHoto: Yusuf Ibrahim Jargaba/DW

Jaridar Der Tagesspiegel ta ruwaito wani dalibi da tun da gwamnati ta saka baki, ya yi sa'ar tserewa daga hannun 'yan bindigar. Mun ji karar harbe-harbe kamar tsawar hadari na kuma tambayi kaina ko za su kashe mu ne domin ba wanda zai tsamanin samun kudi daga dalibi wanda da ma talaka ne, wannan dai shi ne kalaman dalibin. Wannan lamarin dai ya sa a tilas wasu jihohin arewacin Najeriya sun rufe makarantun kwana, abin da ko shakka babu zai kara mayar da hannun agogo baya a harkar ilimi a yankin da yake sahun baya idan aka kwatanta da kudancin kasar.

'Yan majalisa sun ba hammata iska 

A Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, an yi dauki ba dadi a majalisar dokokin kasar da ke birnin Kinshasa. A labarin da ta buga kan batun jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta ce shugaban kasa Felix Tshisekedi ya hau kan karagar muki ne sakamakon wata yarjejeniya da suka kulla da magabacinsa Joseph Kabila, amma yanzu yarjejeniya ta rushe, abin da ke barazana ga kwarya-kwaryar zaman lafiya da kasar ta samu. A makon da ya gabata 'yan majalisa sun ta jifan juna da kujeru. Magoya bayan Kabila sun ja daga a hawa na farko na ginin yayin da masu marawa Shugaba Tshisekedi suka fake a kasa. Mutane da dama sun ji rauni. Kwango dai ta dade tana fama da rikicin siyasa, amma na baya bayan nan ya samo asali ne bayan matakin da Shugaba Tshisekedi ya dauka na rushe kawance tsakanin jam'iyyarsa da ta Kabila bisa dalilin cewa babu wani abin kirki da kawance ya kulla wa kasar.

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW

Karin labarai daga DW