Sharhunan jaridun Jamus 14.03.2023
April 14, 2023Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta yi game da tsamin danganta da ya kunno kai tsakanin kasar Chadi da Jamus. A sharhin da ta yi mai taken "Damuwa da yawa, tsoma baki da yawa", jaridar ta ce, Chadi ta zama wata kasa mai sarkakiya ga kasashen yammacin duniya. Ta ce a daidai lokacin da jakadan Jamus a Chadi Gordon Kricke ya isa birnin Berlin bayan da aka koro shi, Ma'aikatar Harkokin wajen Jamus ta gayyaci jakadar Chadi a kasar Maryam Ali a ranar Talata domin dibar mata wa'adin sa'o'i 48 don ta tattara nata ya nata ta bar kasar.
Franfurter Allgemeine Zeitung ta ce, gwamnati a Chadi ta bayyana a fili cewar ta gaji da suka kan tauye hakkin tafarkin dimokradiyya da jakadan Jamus ke yi mata. Sai dai ta ce a fili yake cewar sojojin gwamnati sun murkushe masu zanga-zanga 128, a lokacin da suke adawa da wani kuduri da ya ba wa Mahamat Idriss Deby damar ci gaba da mulki na wasu shekaru biyu. Jaridar ta kara da cewa Chadi da ta kasance karkashin mulkin kama-karya na tsawon shekaru 31, ta zama kasa mai rikitarwa ga kasashen Yamma, a daidai lokacin da ake fuskantar sukurkucewar dangantaka da gwamnatocin mulkin soja a Mali da Burkina Faso da Guinea tun bayan da suka kakkange madafun iko bayan da suka yi juyin mulki.
Ita kuwa jaridar Berliner Zeitung ta yi sharhi ne mai taken "Ficewa sojojin Jamus daga Mali tare da fadadawa Nijar" a yayin da ministocin Jamus biyu suka ziyarci yankin Sahel. ta ce, Ministan tsaron Jamus Boris Pistorius da Ministar raya kasa Svenja Schulze sun karfafa manufar kasarsu a yankin Sahel gabanin fara janyewar sojojin Bundeswehr daga Mali. Jaridar ta ce, gwamnatin Jamus na son janye sojojinta fiye da 1100 daga aikin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya daga Mali, sakamakon daga rigima da ta kunno kai tsakaninta da shugabannin mulkin sojar kasar. Berliner Zeitung ta kara da cewa tun bayan juyin mulkin Mayun 2021, shugaban gwamnatin rikon kwaryar Mali ya tagayyara aikin rundunar MINUSMA bayan da ya nemi hadin gwiwar Rasha a yaki da masu kishin addini.
Sharhin ya ce, yankin Sahel na daya daga cikin mafi talauci a duniya, wanda kuma ayyukan ta'addanci ya fi shafa, lamarin da ya sa adadin 'yan gudun hijira ya ninka sau goma a cikin shekaru goma na baya-bayannan. Amma dai jaridar Berliner Zeitung ta ce minista Schulze da ke kula da raya kasar a Jamus Jamus ta jajirce wajen kawo wa 'yan yankin Sahel dauki domin rage talaucin da ke sa su fadawa tarkon ayyukan ta'addanci.
Idan muka koma jaridar WELTplus kuwa, ta yi tsokaci ne kan abin da ta kira "Barazana ga kowace al'umma" - da Shugaba Putin na Rasha ke da shi a Afirka wanda ba a sani ba. Ta fara labarin ne da cewar angizon da Rasha ke kara samu a yankin Sahel ya dade yana damun kasashen yammacin duniya. Amma karfafuwar dangantaka tsakanin Aljeriya da Rasha na zama hadari ga manufofin kasashen yammacin duniya.
Jaridar ta ruwaito cewar, mafi yawanci makaman da Aljeriya ke amfani da su sun fito ne daga Rasha. Amma dangantakarsu ba ta samu asali daga yakin Ukraine ne, amma Aljeriya na da dadaddiyar alaka da suke fata dorewarta. A daya hannun kuwa, Rasha tana ba da shawarwarin siyasa ga Aljeriya baya ga goyon bayan matsayinta a rikicin yankin yammacin sahara. Sannan Rasha ta amince Aljeriya ta mika bukatar zama memba a kungiyar BRICS, da ke zama kishiya ga Kungiyar G 7. Saboda haka jaridar ta ce ba a yi mamaki da Aljeriya ta kaurace wa kudirin Majalisar Dinkin Duniya Kuri'u na la'antar mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine ba.
Za mu karkare da ruguntsumin masarautar Eswatini da ya sha suka daga jaridar Der Tagesspiegel karkashin sharhi mai taken "Shekaru 50 na ta'addancin gwamnati a Eswatini". Ta fara ne da dasa ayar tambaya, inda ta ce yaushe ne Sarki Mswati III zai 'yantar da mutanensa? ta kara da cewa sarkin wannan mitsitsiyar kasa ya sake haramta duk wani na nuna adawa ga gadonsa na sarauta. Wannan dai ba farau ba ne, inda na wannan Talata ya kasance karo na 50 a daidai lokacin da ake bikin zagayowar ranar ‘yan adawa.
Duk da cewa ya Sarki Sob huza II da ya gabata ne ya soke tsarin jam’iyyu tun a 1973, amma Sarki Mswati III. da ke ci a yanzu yana ci gaba jefa kasar da ke tsakanin Mozambik da Afirka ta Kudu cikin rikci. Jaridar Der Tagesspiegel ta ce ana kashe duk wani mai sukar Sarki, yayin da daya hannun sarki da matansa 12 na tattara motocin alatu kirar Jamus, yayin da yawancin al'ummar masarautar na rayuwa cikin mawuyacin hali. Har yanzu ba a gudanar da tattaunawar siyasa da aka yi alkawari ba. Maimakon haka yana shirya nada ‘yan majalisar dokokin kasarsa ba tare da la'akari da takaran 'yan adawa ba.