1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Sharhunan Jaridun Jamus 21.06.2024

Ahmed Salisu AH
June 21, 2024

Jaridun na Jamus sun ambato kusan dukkaninsu batun karin wa'adin mulki da shugaban Afrika ta Kudu Cyril Ramaposa ya samu bayan yin kawance da babbar jam'iyyar adawar kasar ta DA da wasu kananan jam'iyyu.

Hoto: Kim Ludbrook/EPA

Bari mu fara sharhunan Jaridun Jamus din da jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung, inda ta gina sharhinta kan karin wa'adin mulki da shugaban Afrika ta Kudu Cyril Ramaposa ya samu bayan yin kawance da babbar jam'iyyar adawar kasar ta DA da wasu kananan jam'iyyu. Jaridar ta ce wannan shi karon farko da wata jam'iyya da ke rinjayen fararen fata ta shiga gwamnati tun bayan kawo karshen mulkin mallaka a kasar. Jam'iyyun adawa irinsu EFF ta Julius Malema sun taya shugaban murna yayin da jam'iyyar MK da tsohon shugaban kasar Jacob Zuma ta kauracewa zaman farko na majalisar tare da shan alwashi ci gaba da kalubalantar zaben da aka yi tare da sukar lamirin kafa gwamnatin hadain kan kas ada aka yi.

Barazanar bacewar wasu al'adun a kasar Mali

Hoto: Kunst- und Ausstellungshalle der Bundesrepublik Deutschland

Bukukuwan al'adu a kasar Mali na fuskantar barazar bacewa. Wannan shi ne taken sharhin da Jaridar Die Tageszeitung. Jaridar ta ce dumamar yanayi na yin barazana ga bikin na na al'ada na shekara-shekara na Sanke Mon wanda kan gudana a watan Yunin kowace shekara. A bikin wanda hukumar UNESCO ta sanya shi cikin jerin bukukuwa masu kayatarwa a duniya ya rage armashi musamman a bana saboda janyewar ruwan da masunta ke amfani wanda ake alakanta hakan ga gurgusowar hamada. Wannan halin da aka shi dai inji mazauna yankin ya shafi tattain arzikinsu saboda mafi akasarin mazauna yankin na dogaro da kogin ne don samun dan abin sayen kayan masarufi.

Shirin gwamnatin Jamus na tasa keyar bakin haure zuwa wata kasar Afirka

Hoto: /dpa/picture-alliance

Jaridar Zeit Online kuwa tsokaci ta yi game da kiran da jam'yyar CDU ta yi na aikewa da bakin haure da ‘yan gudun hijirar Afrika zuwa wata kasa ta dabam da ba ta cikin Kungiyar EU domin tantancesu kafin a ba su mafaka. Wannan batu inji jaridar zai haifar da zazzafar muhawara a taron frimiyoyin jhohi na kasar, musamman kann irin tsarin da za a bi wajen fidda bakin hauren da 'yan gudun hijira daga Jamus zuwa wata kasa ta dabam kafin tantancesu da nufin basu mafaka ko akasin haka. Wannan tsari dai inji Zeit Online din ya yi kama da wanda Birtaniya ta bijiro da shi na aikewa da masu neman mafaka zuwa Ruwanda don tantancesu duk kuwa da cewar kotu ta hana yin hakan. Masu maraba da wannan tsari na ganin hakan zai taimaka wajen rage yawan masu neman mafaka a Jamus.

Alhazai da dama sun rasa rayukansu a lokacin aikin haji na bana saboda zafin rana

Hoto: Rafiq Maqbool/AP Photo/picture alliance

Bari mu kitse sharhin na jaridun Jamus da Jaridar Welt Online wadda nata sharhin ya mayar da hankali kan Alhazai na wasu kasashen Afrika da suka hada da Senegal da Tunisiya da kuma Masar da suka rasu yayin aikin hajjin bana. Jaridar ta ce daga cikin adadin Alhazan da aka bayar da labarin rasuwarsu, 600 sun fito ne daga Masar kuma tsananin zafin da aka yi wanda ya haura maki 50 a ma'aunin Cesius ne sanadin rasuwarsu. Wannan adadi na Alhazan da suka rasu saboda zafin rana inji jaridar shi ne mafi muni da aka ‘yan shakrun baya bayan nan.