1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Sharhunan jaridun Jamus 24.11.2023

Zainab Mohammed Abubakar M. Ahiwa
November 24, 2023

Daga cikin abubuwan da jaridun na Jamus suka duba a Afirka, akwai batun yarjejeniyar Jamus da Najeriya kan samar makamshi a tsakaninsu da ambaliya a gabashin Afirka.

Olaf Scholz na Jamus da Shugaba Tinubu na Najeriya
Olaf Scholz na Jamus da Shugaba Tinubu na Najeriya Hoto: Nosa Asemota/Nigeria State House/AP/picture alliance

Kamar yadda aka saba, jaridun na Jamus sun yi nazarin muhimman batutuwa da suka danganci Afirka a wannan mako mai karewa, amma baru mu fara da labarin da jaridar Der Tagesspiegel wallafa mai taken "Jamus da Najeriya sun amince kan samar da iskar gas".

Jamus za ta dogara da Najeriya don samar da kashi biyu cikin 100 na iskar gas da kasar nan gaba. A daya hannun kuma, Jamus ta amince da zuba jarin dala miliyan 500 a ayyukan samar da makamashin da ake sabuntawa, a cewar jaridar.

Kasashen biyu sun cimma wannan yarjejeniya ta fahimtar juna ne a birnin Berlin a farkon wannan makon, a bangaren taron hadin gwiwa tsakanin Jamus da wasu kasashen Afirka da kungiyar kasashe masu ci gaban masana'antu na G20, mai suna "Compact with Africa" a Turance.

Tuni dai aka rattaba hannu tsakanin kamfanin Najeriya na Riverside LNG da ke yankin Niger Delta da takwaransa na Jamus mai suna da Johannes Schuetze Energy Import. A karkashin shirin wanda za a fara a shekarar 2026, Najeriya za ta bai wa Jamus ton 850,000 na makamashi a ko-wace shekara, kana daga bisani za a fadada shi zuwa ton miliyan 1.2  in ji shugaban kamfanin GasInvest, David Ige kuma daya daga cikin masu rattaba hannu a yarjejeniyar fahimtar junan na kasashen biyu.

Ta'adin ambaliya a kasar SomaliyaHoto: Feisal Omar/REUTERS

"Ruwan sama kamar da bakin kwarya a ya haddasa barna mai tsanani a kasashen Somaliya da Habasha da kuma Kenya" wannan shi ne taken labarin da jaridar Die Zeit ta wallafa kan halin da wadannan kasashe suka tsinci kansu ciki.

A cewar jaridar mutane 124 suka rasa rayukansu a yankin kusurwar Afirka ya zuwa yanzu, daura da gine gine da suka salwanta, sakamakon ruwa sama kamar da bakin kwarya babu kakkautawa ya zuwa yanzu, acewar alkaluman Majalisar Dinkin Duniya. Rahotanni sun ce an gano gawarwakin mutane 50 a Kenya, 41 a Somaliya da kuma 33 a Habasha.

Ruwan sama mai yawa, wanda aka alakanta da sauyin yanayi da duniya ke fuskanta da kuma ruwan da ke kwarara daga tsaunukan Habasha zuwa kogin Somaliyan da ke hadewa da tekun Indiya.

Wajen mutum dubu 649 ne suka kaurace wa gidajensu a Somaliya sakamakon ambaliyar da wasu 371,300 a Habasha kana mutane 121,505 a Kenya, su ma sun rasa matsugunnansu.

Wasu al'umomi a Jamhuriyar Dimukuradiyyar KwangoHoto: Guerchom Ndebo/AFP

Daga batun ambaliyar ruwa a kusurwar Afirka sai cutar kwalara a kasar Zimbabwe da ke yankin kudancin Afirka. Jaridar die Tageszeitung ta ce annobar da ta fi kamari a cikin shekaru kusan goma sha biyar tuni ta yi ajalin daruruwan rayuka.

Adadin wadanda suka rasu daga cutar kwalara ya kai 209. Jaridar ta ruwaito hukumomi na cewa da akwai mutane 8,239 da ake zargi sun kamu da cutar, daga adadin an tabbatar da 1,301 bayan gudanar da gwaje-gwaje. Yanayin dai ya haifar da tsoro a zukatan al'umma da hukumomi, cutar da ake ganin za ta iya yaduwa zuwa wajen Zimbabawen.

Samun ruwa mai tsafta na daya daga cikin abubuwan da ake bukata cikin gaggawa, in ji John Roche, shugaban kungiyar agajin kasa da kasa ta Red Cross na Malawi da Zambia da Zimbabwe, yana mai neman taimakon gaggawa na dalar Amurka miliyan 3.4 don tallafawa kungiyar agaji ta Red Cross ta Zimbabwe.