Jaridun Jamus: Ambaliya a Mokwa, Najeriya
June 6, 2025
Bari mu fara da jaridar die tageszeitung da ta rubuta sharhinta mai taken: Daruruwan mutane sun halaka a Najeriya sakamakon ambaliyar ruwa. Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya yi sanadiyyar rayukan mutane da dama a kusa da Kogin Niger, kulluma ana tono gawarwaki. Shin Ayyukan Hukumar Kula da Kare Afkuwar Bala'o'i ta Najeriya bai yi tasiri ba ne?
Jaridar ta ce garin Mokwa da ke tsakiyar jihar Niger a yankin Arewa maso Tsakiyar Najeriya na cikin alhini, a yanzu garin ya zama mazaunin manya-manyan kaburbura da aka binne gawarwaki tare da zama wajen da matsalar da ke da nasaba da sauyin yanyi ta kafa tarihi. Ana fargabar kimanin mutane 700 sun halaka, bayan ambaliyar ruwan ta baya-bayan nan da ke zama mafi muni a tarihi. Tuni dai aka tabbatar da mutuwar kimanin mutane 200, an kuma dakatar da ayyukan ceto duk da cewa akwai daruruwan mutane da ba a gano ba.
Ita kuwa jaridar Welt online ta rubuta nata sharhin ne mai taken: Shugaban Amurka Donald Trump ya haramtawa 'yan wasu kasashe shiga kasarsa, kamar yadda ya yi a mulkinsa na farko. Jaridar ta ce kasashe da dama na nahiyar Afirka da kudancin Amurka ne haramcin ya shafa, abin da ake fargabar zai iya shafar daliban wasu kasashen na dabam in har suna karatu a jami'ar Havard. Kasashe 12 ne shirin na Trump ya shafa da suka hadar da Afghanistan da Myanmar ko Bama da Chadi da Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da Equatorial Guinea da Iritiriya da Haiti da Iran da Libiya da Somaliya da Sudan da kuma Yemen.
Baya ga haramcin da aka sanya ga al'ummomin wadannan kasashe da zai fara aiki a ranar Litinin da ke tafe, an kuma tsaurara matakan shiga Amurkan ga al'ummomin kasashen Burundi da Kuba da Laos da Saliyo da Togo da Turkmenistan da kuma Venezuela. Matakin na Trump dai, na da alaka da mummunan harin da aka kai kan Yahudawa da ke zanga-zangar lumana a jihar Colorado da ke Amurkan wanda ya yi sanadiyyar raunata Yahudawan 12.
Ba mu sake komawa ga jaridar die tageszeitung da za mu karkare da sharhinta mai taken: Shugaban mulkin kama-karya na Burundi ya kira zaben 'yan majalisun dokoki, zaben da ke gudana ba tare da kwakkwarar adawa ba. Yayin da ake fama da zaman tankiya a yankin, Shugaba Évariste Ndayishimiye ya kaddamar da jerin zabubbuka. Jaridar ta ce: Ana tsakiyar zaben, Hukumar Samar da Wutar Lantarki ta sanar da matsalar katsewar hasken wutar lantarki, abin da ya haifar da shakku kan sahihancin sakamakon zaben.
Bayan zaben 'yan majalisar wakilai a wannan wata na Yuni, za kuma a gudanar da na 'yan majalisar dattijai a watan Yulin da ke tafe kana a gudanar da zaben kananan hukumomi a watan Agusta sai kuma na shugaban kasa a watan Mayun 2027. Akwai dai tababa kan yiwuwar jam'iyya mai mulkin ta CNDD-FDD ta lashe zabukan. Tun dai bayan yarjejeniyar sulhu da suka cimma a 2005, jam'iyyar ta CNDD-FDD da ta bulla daga tsohuwar kungiyar tawaye ta Hutu ke mulki a Burundi, inda shugabanta Pierre Nkurunziza ya mulki Burundi har zuwa shekara ta 2020 da ya rasu sakamakon annobar corona. Tun daga wancan lokaci kawo yanzu, Shugaba Ndayishimiye ya dare kan madafun iko.