1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jaridun Jamus kan nahiyar Afirka

Lateefa Mustapha Ja'afar RGB
July 19, 2019

Cimma gwamnatin hadaka a Sudan da gurfanar tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu a gaban kwamitin bincike kan zargin cin hanci da kuma mutuwar Johnny Clegg su suka mamaye jaridun Jamus.

Sudan Khartoum | Friedensgespräche
Hoto: picture-alliance/AA/M. Hjaj

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung a sharhinta mai taken: Mutane 11. A Sudan 'yan adawa da sojoji sun amince da kafa gwamnatin rikon kwarya ta dimukuradiyya. Jaridar ta ce bayan kwashe tsawon watanni ana tattaunawa, jagororin gwagwarmayar 'yan adawa da ke kiran kansu da "Dakarun kwatar 'yanci da kawo sauyi" da gwamnatin mulkin soja da ke mulki tun bayan kifar da gwamnatin Omar Hassana al-Bashir sun yi nasarar cimma yarjejeniya a Khartoum babban birnin kasar a ranar Larabar da ta gabata. Yarjejeniyar ta amince da kafa gwamnatin hadaka tsakanin bangarorin biyu, inda ko wanne bangare ya bayar da mutane biyar suka kuma amince da wakilin farar hula guda, abin da ya bayar da damar kafa kwamiti mai wakilai 11. Wannan ya sanya a karshe fararen hula suka samu rinjaye a gwamnatin rikon kwaryar hadakar da za a kafa. Za a gudanar da zabe bayan watanni 39 a kasar, domin zabar sabuwar gwamnatin dimukuradiyya. Za a nada ministoci, wadanda jagororin zanga-zangar ne za su bayar da sunayensu. Rarraba mukamai tsakaninsu na daga cikin tanade-tanaden yarjejeniyar da suka sanyawa hannu, nan gaba kadan kuma za a amince da sabon kundin tsarin mulkin kasar.

Jacob Zuma ya musanta zarge-zargen cin hanci da rashawaHoto: Reuters/N. Bothma

Sa'o'i biyu na girgiza, inji jaridar Berliner Zeitung . Jaridar ta ce Jacob Zuma ya musanta baki dayan zarge-zargen da ake masa na al'mundahana da kudin al'umma, baya ga batun kyale iyalan Gupta da ake zargin Zuman na da aminci da su, su warwarasa da dukiyar kasar, inda ya bayyanasu a matsayin son bata masa suna kawai. Tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudun, ya dauki kansa a matsayin wanda ya fada tarkon masu leken asiri. 'Yan jarida sun yi sammako tun da duku-duku domin a tantance su a basu izinin shiga inda Zuman zai bayar da ba'asi, wurin zama dan kadan aka warewa al'ummar kasar masu son ganin kwakwaf. Sauran da suka halarta sun kwashe tsawon sa'o'i a tsaye a gaban ofishin da Zuma ke bayar da ba'asin a birnin Johannesburger na Afirka ta Kudun a ranar Litinin. Kafin tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudun Jacob Zuma ya halarci zaman kwamitin binciken, sai da ya gindaya sharudda da suka hadar da sanin irin tambayoyin da za a yi masa, sai dai ba a ba shi wannan damar ba. Hakan ce ta sanya tunanin ba zai yadda ya halarci zaman kwamitin ba. Sai dai Zuma ya zargi mambobin kwamitin da nuna son kai da zabar bari guda. Zargin al'mundahana da dukiyar kasar ne dai ya yi sanadiyyar yin awon gaba da kujerar mulkin tsohon shugaban Afirka ta Kudun Jacob Zuma ke kai. A karshe ma dai Zuma ya janye bayar da ba'asin, sakamakon abin da ake dangantawa da tambayoyin da ake masa sun yi tsauri da yawa.

Johnny Clegg ya taka rawa a fafutukar kawar da wariya launin fata a Afrika ta KuduHoto: Getty Images/D. Kitwood

Ita kuwa jaridar Süddeutsche Zeitung ta rubuta sharhinta mai taken: Gwagwarmayar samun daidaito. Jaridar ta ce mawaki mai gwagwarmayar yaki da wariyar launin fata Johnny Clegg ya rigamu gidan gaskiya. Ta ce zai kasance lokaci ne na rayuwarsa, akalla rayuwarsa a matsayin mawaki. Johnny Clegg ya taba bayyana haka a birnin Frankfurt na Jamus a shekara ta 1991, yayin da yake karanta taken marigayi Nelson Mandela, cikin wakar da Clegg din ya rubuta lokacin da Mandelan ke tsare a gidan kaso, mai taken "yana tsare" "Ba za mu iya ganinsa ba" shi ne abin da "Asimbonanga" ke nufi cikin harshen Zulu. Clegg ya taimaka wajen tabbatuwar mafarkin 'yan Afirka ta Kudu ta hanyar waka. Ya yi waka da ke adawa da nuna wariyar launin fata, yana waka tare da bakaken fata a yayin da aka haramta hakan, yana buga taken masu rajin yaki da wariyar launin fata da gangarsa. Clegg ya rasu a ranar Talata yana da shekaru 66 a duniya a birnin Johannesburg na Afirka ta Kudu bayan ya sha fama da rashin lafiya. Mutuwarsa ta sake hada kan al'ummar kasar, inda suka hadu baki daya wajen yin jimami. Ana yi masa lakani da "white Zulu" wato dan kabilar Zulu farar fata musamnman a kasashen Turai, kasancewar yana yin shigar 'yan Afirka kana ya kada jitarsa tamkar bakar fata. Sai dai Clegg ba ya son wannan lakani, domin a ganinsa shi ma wani salo ne na goyon bayan nuna wariyar launin fatar da 'yan Afirka ta Kudu ke yi, abin kuma da yake yaki da shi.