1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shari'a kan sakamakon zaɓen Kenya

Usman ShehuMarch 29, 2013

Dan takarar shugaban kasa Raila Odinga wanda sakamakon zaɓe ya nuna cewa ya sha kaye, shi ya shigar da kara, inda ya yi zargin maguɗin zaɓe.

Kenya's Prime Minister Raila Odinga (C), flanked by members of the Coalition for Reforms and Democracy (CORD), addresses the media outside his office in the capital Nairobi, March 16, 2013. Kenya's defeated presidential contender Odinga filed a legal challenge to his election loss on Saturday in a major test of the country's democratic system five years after a disputed vote triggered deadly tribal clashes. REUTERS/Thomas Mukoya (KENYA - Tags: POLITICS ELECTIONS CRIME LAW)
Raila OdingaHoto: Reuters

Ranar Asabar ce wa'adin makonni biyun da tsarin mulkin kasar Kenya ya tanada domin tantance koke-koken da suka shafi zabukan kasar da ya gabata a farko farkon watan Maris nan ke cika, inda kotun kolin kasar za ta yi anfani da damar wajen yanke hukunci game da sahihancin nasarar da hukumar zaben kasar ta sanar na cewar Uhuru Kenyatta ne zai kasance shugaban kasar Kenya na gaba.

Sabon tsarin mulkin da Kenya ke yin anfani da shi dai ya tanadi cewar duk wani dan kasar da ke da korafi akan zabe, yana da 'yancin gabatar dashi a gaban kotu cikin tsukin kwanaki bakwai bayan sanar da sakamakon karshe na zaben.

'Yan takara kalilan da suka hada da Raila Odinga daya sha kaye a zaben shugaban kasar ta Kenya a hannun Uhuru Kenyatta ne suka yi anfani da damar wajen garzayawa zuwa kotun kolin domin samun adalci.

Kawancen jam'iyyun da suka marawa Odinga baya a zaben shugaban kasar, na ganin cewar an sake zaluntar su ne a zaben kamar dai yanda ya faru a shekara ta 2007, lamarin daya sa Lauyan shi Odinga wato Amos Wako ya shaidawa wani gangami a birnin Nairobi cewar a yanzu an sha su sun warke:

Willy Mutunga mai sauraron ƙarar a kotun ƙolin ƙasarHoto: AFP/Getty Images

"Mun kwana da sanin cewar an tafka magudi a zaben kamar dai na shekara ta 2007, kuma ba za mu sake yarda mu bada kai ba a wannan karon."

Raila Odinga dai zai sami damar fayyacewa kotun kolin dalilansa na neman yin watsi da sakamakon daya baiwa Kenyatta nasara, kamar yanda ya tsara a cikin takardun shigar da karar daya gabatarwa kotu, wanda ke nuna rashin mutunta doka a hanyar da hukumar zaben kasar ta bi wajen amincewa da sakamakon, bayan sauya tsarin zaben.

Sai dai kuma wasu manazarta game da harkokin siyasa a Kenya irin su Macharia Munene na da ra'ayin cewar ba wai Raila Odinga na fatan ganin kotu ta soke zaben ne gaba daya ba, amma ya bayar da hujjojin da za su dasa ayar tambaya game da nasarar da Kenyata ya samu ne:

"Idan har sake kidaya kuri'un zai nuna cewar Uhuru Kenyatta zai rasa kimanin kuri'u dubu takwas, to kenan zai gaza samun kashi 50 cikin 100 na sakamakon zaben. Watakila sai kotu ta yanke hukuncin cewar za'a gudanar da zagaye na biyu na zaben shugaban kasa."

Idan ma akwai yiwuwar Raila Odinga zai sami sukunin darewa bisa kujerar shugabancin Kenya, to, kuwa hakan zai kasance ne bayan zagaye na biyu, inda zai yi fatan samun kuri'un da masu zabe suka jefawa sauran 'yan takara a zagaye na farko.

A yanzu dai Odinga ya samu nasarar farko a korafin daya gabatar, a ranar Litinin da ta gabata, yayin da kotun kolin kasar ta ta bayar da umarnin sake kidaya kuri'u a mazabu 22 cikin mazabun kasar 291.

Magoya bayan Odinga a fusace bayan an sanar da sakamakon zaɓeHoto: Reuters

Ko da shike ba wai Odinga ne kadai ya gabatar da kukan zargin tafka magudin ba, amma kotun ta yi watsi da wani zargin da wata kungiyar farar hula da ke fafutukar tabbatar da shugabanci na gari, mai suna African Centre for Open Governance ta gabatar, bisa abinda daya daga cikin alkalan kotun kolin Ibrahim Mohammed ya ce rashin mutunta wa'adin makonni biyun da tsarin mulki ya tanada:

" Da dai a ce masu gabatar da ka'ar sun mikawa kotu takardar neman izinin shigar da ka'rar cikin wani kayyadadden lokaci ne, kuma gabannin ranar zaman sauraron ka'ar, to, akwai yiwuwar amincewa da bukatar su, amma a yanzun nan da ake batu babu wata takarda a gaban kotu da ke neman hakan."

Hukumar zaben kasar Kenya dai ta yi hasashen yin anfani da kwanaki bakwai zuwa goma domin tantance masu zaben da aka yiwa rajista a tashoshin zaben kasar da suka kai dubu 33 da 400.

Mawallafi: Phillipp Sandner/Saleh Umar Saleh
Edita: Pinaɗo Abdu Waba