Shari'a waɗanda suka yi fyaɗe a Indiya
January 3, 2013Talla
Mutanen guda shidda waɗanda galibi suke yin rayuwa a yankunan na yaku bayi na birnin New Delhi na iya fuskantar hukumcin kisa idan aka same su da laifi.Sai dai rahotannin na cewar ɗaya daga cikin su wanda ake kyautata zaton cewar bai kai mizanin fuskantar shari'a ba saboda bai cikka shekaru 17 da haifuwa ba,yanzu haka likitocin na gudanar da gwaje gwaje a kan sa domin haƙiƙance addadin shekarunsa.
Masu aiko a rahotannin sun ce babu wasu lauyoyi da suka fito cewar zasu kare waɗannan matasa a gaban shari'a.Kisan dai na dalibar yar shekaru 23 ta hanyar fyaɗe da dukan da suka yi ma ta a cikin wata motar bus a makon jiya, na ci gaba da janyo jerin zanga zanga a ƙasar ta Indiya.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Saleh Umar Saleh