Shari'a wasu 'yan fashin jiragen ruwa na Somaliya a Holland
June 17, 2010Wata kotu a ƙasar Holland ta yanke wa wasu 'yan ƙasar Somaliya su guda biyar 'yan fashin jiragen ruwa hukumci ɗaurin shekaru 5 na zaman gidan yari.Kotun dai ta samu 'yan ƙasar ta Somaliya masu kimanin shekaru 25 zuwa 45 da laifin kai hari akan wani jirgin ruwan Turkiya a gaɓar ruwan tekun Aden. Wannan dai shine karo na farko da aka yiwa yan fashin na ƙasar Somaliya sharia'a a nahiyar Turai.Pottengal Mukundan shugaban wata ƙungiyar da ke fafutukar yaƙi da 'yan fashin da ke a London yayi tsokaci kamar haka.
Abinda ke da mahimmanci ba wai kwai a tsaya akan yan fashin ba dake fashin jiragen ruwa kamata ya yi a yi kokarin kamo masu talaffamasu da kudi wanda kuma suke shirya hare haren da suke kaiwa a kan jiragen ruwan domin a hukumtasu.
Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Eidita : Ahmad Tijani Lwal