Shari'ar Habré a Senegal
July 20, 2015A wannan Litini ne, kasar Senegal ke shirin fara shari'ar tsohon shugaban kama karyar Chadi Hissene Habre, shekaru 25 da ficcewarsa daga kasar, bayan mulkinsa na shekaru takwas, wanda ake zargi ya zubar da jinin fararen hula ya kuma ci zarafin mutane da dama.
Mai shekaru 72 ya kasance a hannun mahukuntan Senegal ne tun bayan da suka cafke shi a gidan da yake zaune da matarsa da 'ya'yansa a birnin Dakar, a watan Yunin shekara ta 2013.
Kungiyoyin kare hakkin bil adama na kiyasin cewa 'yan Chadi sama da dubu 40 ne aka kashe daga shekarar 1982 zuwa 1990, a karkashin mulkin nasan da ya rika murkushe 'yan adawa da kabilun da ake kyautata zaton sun kasance barazana ga gwamnati.
Da yawa na ganin cewa wannan shari'a za ta kafa tarihi saboda kafin yanzu, kotunan kasa da kasa ne ke sharia'ar duk shugabanin Afirkan da ake zarge da tafka miyagun laifuka. A shekara ta 2012 ne dai Senegal da Kungiyar Tarayyar Afirka suka kulla wata yarjejeniyar da ta girka wannan kotun da zata yanke wa Habre hukunci.