Shari'ar kisan Kim Jong Nam a Malesiya
October 2, 2017Mata biyu da ake tuhuma kan zargin kisan Kim Jong Nam dan uwan Shugaba Kim Jong Un na Koriya ta Arewa, sun bayyana a gaban kotu a ranar Litinin din nan saii dai sun musanta zargin hannu a kisan.
Doan Thi Huong, 'yar shekaru 29, daga Vietnam, da Siti Aishah 'yar shekaru 25daga Indunusiya ana zargin sun shafa wani sanadari mai hadarin gaske a fuskar Kim, dan uwan shugaban na Koriya ta Arewa mai shekaru 45 a filin jiragen sama na Kuala Lumpur a watan Fabrairu, ya kuma rasu ne sa'oi kadan bayan shafa masa wannan sinadari.
Masu gabatar da kara a Malesiya sun bayyana cewa za a gabatar da shedu tsakanin 30 zuwa 40 a gaban kotu yayin da kwararu goma suma za su bayyana. Idan har ta tabbata wadannan mata biyu na da hannu a kisan na Kim za su iya fuskantar hukuncin kisa.