Najeriya ta gaza nasara kan Malabu
June 15, 2022Bayan kwashe shekaru ana tafka wannan shari'a amatakai dabam-dabam a kan rijiyar mai lamba 245 da aka yi wa lakabi da badakalar Malabu ne dai, Najeriyar ta ci karo da wannan sakamako a kotun. Wannan hukuncin dai, ya sanya Najeriyar tafka asarar makudan kudi. Najeriyar ta nufi kotu ne kan zargin cewa kamfanin JP Morgan ya yi ganganci, wajen biyan tsohon ministan mai na kasar Dan Etete dala miliyan 875 a asusunsa. Mahukuntan na Abuja sun nuar da cewa kudin da aka biya tsohon ministan man kudi ne na gwamnati, a dangane da haka suke bukatar a biya gwamnatin dala bilyan daya da miliyan 500. Sai dai kotun da ta saurari karar a birnin London na Birtaniya, ta ce Najeriyar ta gaza nuna gamsasshiyar shaidar cewa an zambace ta.
Badakalar wannan rijiyar mai ta samo asali tun daga lokacin da Dan Etete ke ministan man fetur din, a zamanin mulkin tsohon shugaban Najeriyar marigayi Janar Sani Abacha. Hakan ya faru ne sakamakon zargin cin hanci da rashawa da aka yi wa Etete a 2011 zuwa 2013. Da yake tofa albarkacin bakinsa kan hukuncin kotun, tsohon ministan shari'a na Najeriyar Mohammed Adoke cewa ya yi sakamakon shari'aa ya wanke shi. An kiyasta cewa wannan rijiyar man fetir mai lamba 245 da ke yankin Niger Delta na da dimbin arzikin mai da ya kai ganga milyan 482, abin da ya sanya badakalar ta dauki hankali sakamkon zargin yin rub da ciki da kudi da kuma yadda aka sayar da ita. Ba wannan ne dai karon farko da Najeriya ke yin rashin nasara tare da tafka asara wajen biyan diyya, a kotunan shari' a na kasa da kasa ba.