Shari'ar Sankara: Daurin rai da rai ga Blaise Compaore
April 6, 2022Kotun soji da ke birnin Ouagadougou ta yanke hukuncin ne shekaru 34 bayan kisan tsohon jagoran juyin juya hali na Burkina Faso Kyaftin Thomas Sankara a juyin mulkin da ya kawo Blaise Compaore kan karagar mulki, wanda yanzu haka yake gudun hijira a kasar Côte d'ivoire.Tun farko Kotun ta bukaci a yanke wa mutanen da aka samu da hannu a kisan hukuncin daurin shekaru 30 na zaman gidan yari.
Amma kotun ta yanke wa Blaise Compore ne hukunci tare da wasu mutane 20,ciki har da janar Gilbert Diendéré, mai shekaru 61 da ke zama daya daga cikin shugabannin sojojin a lokacin da aka yi juyin mulkin a shekara ta 1987.Compaore wanda boren jama'a ya kora daga mulki a shekarar 2014, ya kasance aboki kana amini na kut da kut ga Thomas Sankara wanda suka yi makaranta tare.
A cikin watanni shida da aka shafe wannan shari'a, shaidu kusan guda 100 ne suka bayyana a gaban kotun domin bayyana abubuwan da suka faru a ranar 15 ga watan Oktoban 1987. Wani soja mai suna Yamba Elisée Ilboudo, ya ce a jajibiren kashe Thomas Sankara, Blaise Compore ya gana da tsohon shugaban a gidansa. Ya ce ya gamsu game da yadda shari'a ta tabbata.
Ya ce: " Eh, mun gamsu bayan shafe shekaru 35 muna jiran shari'a, kotu ta saurari shaidu kusan dari da lauyoyi da farar hula kusan ashirin, mun samu labarin cewa an dade ana shirin kulla makircin, wanda aka kula makarkashiyar a gidan Compaore kafin su zo su taras da Sankara da tawagarsa a fadarsa su bude masa wuta."
Ana zargin wasu daga cikin shugabannin Afirka da hannu a kisan musamman ma tsohon shugaban Côte d'ivoire Félix Houphouët Boigny, wanda wasu shaidu suka gabatar a matsayin wanda ya kitsa makarkashiyar da aka yi wa jagoran juyin juya hali na Burkina Faso.
Yamba ya ce da Blaise Compaore ya ba da shaida da za a san abubuwa da yawa, inda ya ce: "Abin takaici ne cewa ba ya nan, domin ya dauki alhaki kan abin da ya aikata. Mun yi nadamar rashin halartar Blaise Compaoré da Hyacinthe Kafando a wannan zaman shari'a."
Cif Hyacinthe Kafando dai, wanda ake nema ruwa a jallo tun shekarar ta 2016, ana zarginsa da jagorantar kwamandojin da suka kashe Thomas Sankara da abokansa.Mai sharia Apollinaire Kyélem ya ce samun yin shariar bayan shekaru 34 babbar nasara ce.
Ya ce: "A nahiyar Afirka babu wanda a kai shari'ar burkina fasdo cikaken 'yancin. Babbar majalisar shari'a ta zama hukuma mai cin gashin kanta daga hukumomin gwamnati. Hukuncin ya kasance ne bisa doka ba tare da bata-gari na siyasa ba."
Yanzu haka dai Balaise Cmpore da iyalensa sun samu mafaka a Côte Divoire inda suka samu takardun zama 'yan kasa. Shin ko za a iya tia keyarsa zuwa Burkina Faso domin fuskantar hukuncin daurin da aka yi masa? Lokaci ne zai tabbatar!
.