1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shari'ar wadanda suka yi yunkurin kifar da gwamnati

Gazali Abdou Tasawa RGB
December 16, 2022

Kotu a Nijar ta dakatar da shariar sojoji da suka yi yunkurin juyin mulki a jajiberin da Mahamadou Issoufou ke shirin mika mulki ga zababben shugaban kasar Mohammed Bazoum.

Shugaba Mohamed Bazoum
An yi yunkurin juyin mulkin a gabanin rantsar da Shugaba BazoumHoto: Presse- und Kommunikationsdienst der Präsidentschaft von Niger

A wannan Juma'ar kotu a Jamhuriyar Nijar ta fara zaman shari’ar sojojin da ake zargi da hannu a yunkurin juyin mulki na ranar 31 ga watan Maris na shekara ta 2020, tuni wasu daga cikin sojojin da ake zargi suka karba laifinsu a yayin da wasunsu suka musanta. Kotun ta dakatar da zaman shari’ar bayan da lauyoyin sojojin da ake zargi suka kalubalanci halascin kotun sojojin a gaban kotun tsarin mulkin kasar.

Mutane sama da 60 ne aka gurfanar a gaban kotun sojojin a bisa zargin kasancewa masu hannu a yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a shekara ta 2020, ana sauran kwanaki biyu a rantsar da sabon zababben shugaban kasar Mohamed Bazoum. Tuni dai wasu daga cikin sojojin da suka gurfana a gaban kotun suka tabbatar cewa da hannunsu a cikin yunmkuri a yayin da wasunsu suka musanta.

Mohamed Bazoum da Mahamadou Issoufou Hoto: Aboubacar Magagi

Wani abin da lauyoyin sojojin da ake zargi suka suka yi korafi a kai shi ne, yadda suka ce alkalin kotun ya haramta masu gabatar da wasu mutane da za su ba da shaida a kansu a yayin da a daura daya ya bai wa masu zargi izinin. Yanzu haka dai takun saka da ya dabaibaye tafiyar da wannan shari’a ya sanya lauyoyin kalubalantar zaman kotun baki daya a gaban kotun tsarin mulki, suna masu cewa, kotun sojojin da kanta ta saba wa kundin tsarin mulkin kasar ta Nijar.

A daren 31 ga watan Maris din 2020 ne, wasu sojoji dauke da manyan bindigogi suka kai farmaki a fadar shugaban kasa inda bayan dauki ba dadi na kasa da awa daya, rundunar fadar shugaban kasar ta murkushe maharan tare da kama da dama daga cikinsu, inda aka yi ta farautar sauransu daga bisani, mutanen da a yanzu aka gurfanar da su a gaban kuliya.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani