1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisa za ta fara shari'ar tsige Trump

Abdullahi Tanko Bala
January 21, 2020

A wannan rana ta Talata majalisar dattijan Amirka za ta fara shari'ar tsige shugaba Donald Trump game da tuhumar da ake yi masa na tursasa wa Ukraine binciken abokin hamaiyarsa Joe Biden da rike kudin tallafi ga kasar.

USA | Trump | Impeachment
Hoto: picture-alliance/dpa/AP Photo/E. Vucci

 Yayin da 'yan majalisar dokokin ke hallara karkashin jagorancin babban mai shari'a John Roberts da zai jagoranci sauraron shari'ar wadda ba kasafai ake yin irinta ba, 'yan majalisar dattijan sun yi rantsuwar bin lamuran bisa gaskiya da adalci.

Lauyoyi masu kare shugaba Trump sun baiyana zargin da ake yi masa da cewa bita da kullin siyasa ne kawai. A waje guda dai shugaban zai tashi zuwa Davos na kasar Switzerland domin halartar taron tattalin arziki na duniya.

A watan da ya gabata 'yan majalisar wakilai na jam'iyyar Democrats sun tsige Trump kan laifuka biyu da ake tuhumarsa na cin amanar matsayinsa tare da rike kudaden tallafi ga kasar Ukraine da kuma hana majalisa gudanar da aikinta