1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shari'ar tsohon shugaban Masar

August 3, 2011

An gurfanar da Hosni Mubarak a gaban kotu bisa zargin cin hanci da gallazawa al'ummar sa-duk da rashin lafiyar daya ke fama da ita

Tsofon shugaban ƙasar Masar Hosni MubarakHoto: picture alliance/dpa

A ranar Laraba aka fara shari'ar tsohon shugaban Masar Hosni Mubarak a birnin alƙahira. Mubarak, wanda boren adawa da gwamnatin sa ya tilasta masa sauka daga mulki a cikin watan Fabrairu, yana fuskantar zarge-zargen da suka shafi cin hanci da rashawa da kuma bayar da umarnin kissar masu zanga-zangar adawa da gwamnati a lokacin daya ke riƙe da muƙamin shugaban ƙasar ta Masar.

Masu zanga-zanga da murnar fara shari'ar MubarakHoto: dapd

An dai ci gaba da tsare tsohon shugaban a yayin da yake kwance a gadon asibiti dake birnin Sharm el-Sheikh tun cikin watan Afrilu, amma kuma ana sanya ran zai bayyana a gaban wata kotu dake birnin alƙahira, fadar gwamnatin ƙasar ta Masar. Shari'ar dai za ta gudana ne a wata makarantar bada horo ta jami'an 'yan sanda saboda dalilan tsaro, kana hukumomin sun tura sojoji da jami'an 'yan sanda dubu ukku ne domin kula da sha'anin tsaro a lokacin shari'ar.

A halin da ake ciki kuma, tashar telebijin ta Masar ta bayyana cewar tuni wani jirgin sama ya ɗauki tsohon shugaban daga Shar el-Sheikh zuwa alƙahira domin shari'ar.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Umaru Aliyu