1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha da Ukraine a gaban ICC

Abdourahamane Hassane
September 18, 2023

Kotun kasa da kasa da ke hukunta manyan laifukan yaki ICC za ta fara sauraran karan da Ukrane ta shigar sakamakon mamayar da Rasha ta yi mata a shekara ta 2022.

Kotun ICC
Kotun ICCHoto: Hollandse Hoogte/ANP/imago images

Wakilan kasashen biyu da ke yakiza su gabatar da hujjojinsu a gaban alkalai a hedkwatar kotun, da ke a birnin Hague.Tun farko shugaban Rasha Vladimir Putin  ya ba da hujjar mamaye Ukraine a ranar 24 ga Fabrairu, na shekara ta 2022 kan zargin kisan kare dangi da Kiev ta shirya a gabashin Ukraine mai magana da harshen Rasha, sai dai Ukraine ta musunta zargi.

Hoto: Peter Dejong/AP Photo/picture alliance