Shari'ar 'yan adawa a Kamaru
May 20, 2025
Wannan al'amari ya jawo cece-kuce tsakanin 'yan siyasa masu mulki da yan adawa wadanda suke sukar juna a Kamaru. Hana Kamto shiga zaben shugaban kasa na watan Oktoba zai iya ta da hankalin magoya bayansa. A gefe guda kuma kauracewa zabukan da ya yi na iya mayar da hannun agogo baya duk da cewa masanin shari'a ne. Louison Essomba ta kungiyar farar hula kuma makusancin jam'iyya mai mulki yana ganin kowacce jami'yya ana zaban wanda zai tsaya takarar zabe, wanda ya zo daidai da dokar zabe.
Karin Bayani:Kamaru: An daure magoya bayan Kamto
Akwai wasu jam'iyyu da ba su shiga zabukan 2020 ba, ko da kuwa suna da sanatoci da shugaban kasa ya nada amma sun gabatar da dan takarar na zaben shugaban kasa inji Sheikh Ali Asade na jam'iyyar MRC akwai matsala.
Maurice Kamto dai a shafinsa na Facebook ya gargadi mahukuntan Kamaru cewa abin da ya faru a zaben 2018 ba zai iya faru ba a 2025, saboda samun zaman lafiya.
Wannan batun zabe ya dauki hankali galibin yan Kamaru harma ranar 15 ga watan da muke ciki ne kotun tsarin mulkin Kamaru ta dage zaman shari'a na fursunoni 23, ‘yan jam'iyyar adawa ta MRC da aka tsare a 2020 da bisa laifin yin zanga-zangar lumana inda suka kalubalanci mulkin shugaban kasa Paul Biya, wanda kawo yanzu suna tsare a babban gidan yarin Nkondengui shekaru 5 ke nan.