1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Siyasar Pakistan: Sharif ya rantsar da majalisar ministoci

March 11, 2024

An rantsar da mutane 19 a matsayin ministocin da za su marawa sabuwar gwamnatin Firaiminsitan Pakistan Shahbaz Sharif, a wani 'dan kwarya-kwaryar biki da aka gudanar a fadar gwamnati dake birnin Islamabad.

Ministoci 19 a yayin da suke karbar rantsuwar kama aiki a Pakistan
Ministoci 19 a yayin da suke karbar rantsuwar kama aiki a Pakistan Hoto: pid.gov.pk

Shugaban kasar Asif Ali Zardari shi ne ya jagoranci rantsar da ministocin a babban birnin Islamabad. Nadin na zuwa ne 'yan kwanaki bayan da kawancen jam'iyyun Pakistan ciki har da babbar jam'iyya mai mulki ta Pakistan Muslim League-N suka amince da zabar Sharif. Sharif ya taba rike mukamin na rikon kwarya daga watan Afrilun 2022 zuwa Augustan 2023, bayan ya maye gurbin babban abokin hamayyarsa Imran Khan.

Karin bayani: Pakistan: Shehbaz Sharif ya zama Firaminista a karo na biyu 

Nan gaba kadan a yau ake sa ran  Firaiminsitan  zai gana da sabuwar majalisar ministocin domin tattauna tarin matsalolin da kasar ke fuskanta kama daga batun tattalin arziki da matsalar tabarbarewar hasken wutar lantarki da kuma alakar Pakistan da makwabciyarta Afghanistan karkashin gwamnatin Taliban.