Sharon yace zai ci gaba da tattaunawar zaman lafiya da Palsdinawa
December 26, 2005Jamiyar Kadima ta Prime ministan Israila, Ariel sharon,ta baiyana a yau din nan cewa,ta yanke shawarar mayar da tattunawar zaman lafiya da Palasdinawa,ya zama daya daga cikin batutuwa mafiyai muhimmanci a gabanta.
Kuriar jin raayin jamaa da aka gudanar kwanan nan,ta nuna cewa akwai alamun cewa sabuwar jamiyar da Sharon ya kafa a watan da ya gabata,zata lashe zaben watan maris mai zuwa.
Wata jaridar kasar mai suna Maariv a yau tace,Sharon ya fice daga jamiyar Likud don ya samu damar ci gaba da tataunawar zaman lafiya da Palasdinawa ba tare da tsangwama ba.
A cewar jaridar ,Jamiyar Kadima tayi imanin cewa ci gaba da tattaunawa da palasdinawa itace kadai hanya da zata samar da zaman lafiya mai dorewa a yankin,tace kuma zata taimaka wajen tabbatar da kafa kasar palasdinu mai yancin cin gashin kanta.