1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shawara ga 'yan tawayen Libiya

Halimatu AbbasApril 21, 2011

Ƙasashen Faransa da Italiya sun ba Birtaniya haɗin-gwiwa wajen taimaka wa 'yan tawayen Libiya da ke yaki da gwamnatin Shugaba Muammar Gadhafi.

Yan tawayen Libiya a garin AjdabiyaHoto: dapd

Ƙasahen Faransa da Italiya sun ba Birtaniya haɗin-gwiwa a shirinta na tura mashawartan aikin soja domin sun taimaka wa 'yan tawayen da ke gabashin Libiya. To amma Amirka ta ce ba za ta ba da tata gudunmuwa ga wannan shiri ba. Faransa ta ce ta tura wasu jami'an hulɗa da za su ba da taimakon fasaha da na aiki da kuma tsari ga 'yan tawayen. Sakataren harkokin wajen Birtaniya, William Hague ya ce ƙasarsa za ta tura mashawaratan aikin soja guda 12 amma ba za su shiga aikin ba da horo ko kuma makamai ga 'yan tawayen ko kuma taimaka masu wajen shirya ayyukansu ba. Ƙungiyar tsaro ta NATO dai ta sha nuna rashin amincewa da tura dakaru ta ƙasa. Shugaban dakarun ƙungiyar, Russel Harding ya yi magana yayin wani taron 'yan jarida inda ya ce ƙungiyar za ta yi aiki ne domin kare farar hula daidai da ƙudurin Masjalisar Ɗinkin Duniya. A dai halin da ake ciki yanzu wasu 'yan jarida biyu sun mutu sakamakon raunukan da suka samu daga harbin bindiga cikinsu har da Tim Hetherington, fitaccen ɗan jarida da ya taɓa samu lambar yabo ta Oscar. Wasu kuma biyu sun samu raunuka.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Ahmad Tijani Lawal