1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arzikiNajeriya

Shawarar IMF don samun karin kudin haraji a Najeriya

Ubale Musa Mouhamadou Awal
June 16, 2026

A wani abin da ke iya kara ta’azzara talauci a Najeriya, Asusun Lamuni na Duniya IMF ya nemi gwamnatin tarayya ta kaddamar da haraji kan man fetur da harkokin sadarwa domin samun karin kudade.

Shugaba Bola Tinubu, da Anwar Ibrahim da Kristalina Georgieva ta IMF
Shugaba Bola Tinubu, da Anwar Ibrahim da Kristalina Georgieva ta IMFHoto: Fayez Nureldine/AFP

IMF ta ce Najeriya na iya samun kudaden da daman gaske daga sabon harajin mai da dakika ta salula da 'yan kasar suke zuka. Amma kwarraru na kasar na jan kunnen Abuja bisa yiwuwar ta‘azzarar talauci sakamakon sabon  harajin da ke zaman al'adda a kasashe da yawa.

A karkashin sabon tsarin, gwamnatin Najeriya na iya samun karin kaso 7,5% a kan kowace litar mai ko kuma dakika ta wayar salula a cikin kasar, abin da a cewar IMF ke iya ba wa mahukunta karin kudin shiga.

Karin bayani: Dokar haraji ta ja takaddama a Najeriya

A bara kadai, Najeriyar ta sha man fetur  da ya kai lita miliyan dubu 19 ko biyan Naira sama da Tiriliyan bakwai na cinikin data da kudin buga waya a shekarar da ta shude. Abuja ta ce tana karkata ga haraji ne a kokarinta na inganta rayuwa ral'ummar kasar.

Shakkun masana kan harajin fetur da sadarwa

'Yan Najeriya na korafi kan talauci sakamakon janye tallafin mai da kakaba harajiHoto: Pius Utomi Ekpei/AFP/Getty Images

Sai dai tun ba'a kai ko'ina ba, bukatar IMF ta fara fuskantar turjiya a ciki tarayyar Najeriya, inda masu kodagon kasar suke fadin cewar akai kasuwa. Dr Abbayo Nuhu, sakataren kungiyar manyan ma'aikatan Najeriya ya ce: "Maganar teburin mai shayi ne, domin kudin da aka samu a tallafin mai da aka zare, me aka yi da shi?.. Ba mu gani a kasa ba, illa kara shiga halin kaka ni ka yi."

Duk da cewa Abuja ba ta kai ga bayyana ra'ayinta kan bukatar IMF ba, amma daga dukkan alamu shawarar ga Shugaba Tinubu, da ya kafa tarihi a batun haraji, ta bata ran 'yan adawa na kasar. A baya, Tinubu ya kau da kai ga karuwar adawa wajen kafa sabuwar dokar haraji ga kasar, wacce ta ba da damar tara kudade ga masu mulki da talauta talakawansu.

Karin bayani: IMF: Najeriya na fama da talauci da hauhawar farashi

Maigari Bello Kasimu, jigo na bangaren adawa ya ce Asususn Lamuni na Duniya na shirin nuna baka ga kuciyar da ta kwashe hatsin talakawa na kasar. Ya ce: " Dama abin da suke nema ke nan, yanzu haka tun da sun hana mu wutar lantarki mun koma solar,  suna  kakaba mana haraji. Sun hana mu ruwan sha, amma duk mun koma tona bohol, suna son kakaba mana haraji."

Sabon harajin zai ta'azzara talauci a Najeriya

Masana suka ce musayar kudi za ta ja baya idan aka yi karin haraji a NajeriyaHoto: Kehindeolufemi/Depositphotos/IMAGO

Ita kanta hukumar IMf ta ce akwai batun talauci cikin kasar kafin sabon juyin da ke nuna alamun rudu a kokarin neman mafita. Farfesa Muttaqa Usman, kwarrare a fannin tattalin arziki ya ce: " Kasar da kashi 63% na al'ummarta ke fama da talauci kamar yadda kididdigar IMF ta nunar, ka ce za ka kara musu haraji? Wannan harajin man fetur na da mastala, saboda duk inda ka sa shi sai ya hau da farashin dukkan abubuwan da suka shafi rayuwar dan Adam."

Karin bayani:Najeriya ta zuba kudaden yaki da talauci a Arewa

Mahukuntan Najeriya na a tsakanin cika aljihu da kudaden haraji, da kuma kara aika talauci cikin gidan talakawa, ko kuma su hakuri da harajin da ma kasa sauke nauyi cikin batun yin mulki.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani