1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shawarar Larabawa ga MDD kan yadda za a kwato Kudus

Mahmud Yaya Azare GAT
February 1, 2018

Ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa sun nemi MDD da ta bullo da wani tsari dai zai aiwatar da kudurorinta kan kafuwar kasar Palasdinu, ba tare da hawa kujeran nakin da Amirka ke yi a majalisar ya yi tasiri ba.

Felsendom Jerusalem
Hoto: picture-alliance/Zumapress/S. Qaq

A taron da ke zama irinsa na farko da Larabawan ke kalubalantar matakin Amurka na maida birnin Kudus ya zama shelkwatar Isra,ila, bayan da a baya suka takaita tarukansu kan yin tofin Allah tsine kadai ga matakin, a wannan karon Larabawan sun nuna alamun yin kazar-kazar da gaske, yadda illahirin ministocin suka amince da kudurin da Falasdinawa suka gabatar, wanda suke ganin zai rage babakeren da Amirka ke yi a yunkurinsu na ganin kafuwar kasarsu mai shelkwata a birnin Kudus.
Saeed Abu Ali, shi ne mataimakin magatakaddar kungiyar kasashen Larabawa, ya kuma bayyana dalilan da suka sanya larabawan daukar wannan matakin:

 “Yin tofin Allah tsine ga matakin da I'sraila ke dauka da ke da matukar hatsari ga birnin Kudus, bayan da Amurka ta halasta mata mallakar birnin ita kadai tilo, wannan mataki na fatar baki ba zai taba wadatarwa ba, don haka ne, muka dau matakin aiki da cikawa, wanda zai taka burki  ga duk wani sabon yunkuri da ya saba doka da Isra,ila da Amirka za su dauka, na sauya tsarin da birnin na Kudus ke ciki tun tun tuni.”

Sameh Shukri, ministan harkokin wajen Masar, wanda ya yabawa Majalisar Dinkin Duniya kan bajintar da ta nuna a taron gaggawar da ta kudanar, na kin amincewa da kwace wa Falalsdinawa birnin Kudus da Isra'ila ke shirin yi, tare da hadin bakin Amirka, ya nemi Majalisar Dinkin Duniyar da ta ci gaba da taka kyakkyawar rawarta kan rikicin na Falasdinu da Isra'ila, don kar tura ta kai Falasdinawan bango:

“Ci gaba da yiwa Falasdinawa karfafa a kasarsu ta gado, kan iya kurar da su, su fara daukar matakan a fasa kowa ya rasa, kamar yadda zai sanya alummar Larabawa su dawo daga rakiyar masu kiraye-kirayen a mai da wuka don a sasanta, su koma bin masu  tsatsauran ra,ayi da wuce gona da iri da ma 'yan ta,adda.”

Hoto: picture alliance/dpa/AP/N. El-Mofty

Wannan taro da ke zuwa a daidai lokacin da nuna kyamar Isra,ila da al'umomin Larabawa ke yi ke karuwa, su kuma wasu shuwagabannin na Larabawa ke kara zakewa wajen kulla alaka ta zahiri da ta badini da Isra'ilar, wasu masharhanta na ganin tamkar wani yunkuri ne na rashin hadin kan al'ummar larabawan, da neman wanke kai da shuwagabannin larabawan ke son yi, gami da yunkurin kaucewa daga daukar nauyin da ya rataya kansu na daukar matakan mai da Isra'ila saniyar ware, da yanke huldar diplomasiya da ta kasuwanci da waunsu ke yi da ita, gami da goyan bayan boren Intifadha da kungiyoyin Falalsdinawa masu fafutuka ke shirin yi, kamar dai yadda ministan harkokin wajen Jodan, Aimanil Safdi ya ce,in da Larabawan za su dauki irin wannan matakin na bai daya da tuni an gama warware rikicin gabas ta tsakiya:

“ Mu nuna musu cewa, nuna kosa da reni da suke mana, gami da keta dokakin kasa da kasa, da yin rub da ciki kan abunda ba nasu ba, zai mai da su saniyar ware a yankinmu, da kuma kara yiwa kansu dabaibayi da makiya da zama cikin damuwa da tashin hankali.”

 

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani