Shawarwarin Ban Ki-Moon ga warware rikicin Masar
July 11, 2013Babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki-Moon ya nuna damuwarsa dangane da yadda ake ci gaba da tsare mutane a Masar da kuma sammacin da aka yi wa jagororin ƙungiyar 'yan uwa Musulmi bayan da sojoji suka hamɓarar da mulkin Muhammad Mursi.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya rawaito cewa, a wata ganawa da suka yi ta wayar tarho, Mr Ban Ki - Moon ya bayyana wa minisatn harkokin wajen Masar Mohammed Kamal Amr cewa, Majalisar Ɗinkin Duniya ba za ta lamunci wani yunƙuri na yin bita da ƙullin siyasa ko kuma ma mayar da wata Jam'iyya ko al'umma saniyar ware ba a Masar.
Haka nan kuma Mr. Ban ya sake nanata goyon bayansa ga kyawawan fatan da jama'ar Masar ke da shi, kuma a dalilin haka ya yi kira ga duk ɓangarorin da abun ya shafa da su gudanar da tattaunawa na sulhu domin samun mafita mai a'ala.
Mr Ban ya yi wa ministan harkokin wajen Masar ɗin tuni dangane da alhakin da ya rataya a kan ƙasar a matakin ƙasa da ƙasa da kuma buƙatar mutunta 'yancin walwala wanjen ma'amala, da faɗin albarkacin baki da kuma mutunta dokokin ƙasa.
Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Saleh Umar Saleh