Shawarwarin maido da danganta tsakanin Amurka da Koriya ta arewa
March 6, 2007Talla
Amurka da Koriya ta arewa na cigaba da tattauanwa a ƙokarin farfaɗo da hulɗar dangantaka a tsakanin su wadda ta yi tsami kusan shekaru 50 da suka wuce. Matainamkin sakataren harkokin waje Amurka Chirstopher Hill da takwaran sa na Koriya ta arewa Kim Kye-Gwan sun isa birnin New York domin tattaunawar. Ƙokarin maido da hulda a tsakanin ƙasashen biyu ta biyo baya yarjejeniyar da aka cimma ne a ranar 13 ga watan Fabrairu a taron ƙasashe shidda wanda ya gudana a Beijin na dakatar da shirin nukiliyar Koriya ta arewa. Kakakin fadar white House Sean McCormack yace Amurka na nazarin cire Koriya ta arewa a jadawalin ƙasashe masu ɗaurewa taáddanci gindi