1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shawarwarin sulhu game da rikicin siyasar Kenya

Tanko Bala, AbdullahiFebruary 27, 2008

Tsohon sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Kofi Annan ya ɗage tattaunawar taron sulhu na sasanta rikicin siyasar Kenya

Tsohon Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Kofi Annan yayin da yake jawabi ga yan Jarida a birnin Nairobi.Hoto: AP

Tattaunawar sulhunta rikicin siyasar ta Kenya ta ci tura ne a ranar Talata sakamakon kwan gaba kwan baya da kuma jayayya a tsakanin ɓangarorin gwamnatin dana yan adawa. Akan haka Kofi Annan wanda ke shiga tsakani wajen sulhunta taƙaddamar ya yanke shawarar ɗage zaman taron ya zuwa wani lokaci nan gaba. " Annan yace tattaunawa na cigaba, to amma ina ɗaukar matakai ne domin tabbatar da cewa mun cimma masalaha cikin hanzari da tsakani fiye da irin takun da aka rika yi makwanni biyu da suka wuce. Tsohon sakataren Majalisar Ɗinkin Duniyar ya yi kira ga shugaba Mwai Kibaki da madugun jamíyar adawa Raila Odinga su baiwa jamián dake wakiltar su a waɗannan shawarwari cikakken jadawali da umarni kan yadda zaá ci gaba idan kuma ba haka to su shigar da kan su a tattaunawar. Yace akwai muhimmanci sosai ga shugabanni su ja ragamar alámura da kan su domin wannan ba batu ne na jamíyun siyasa ko bukatu na wasu ba, lamari ne da ya shafi alúmar Kenya dama yankin baki ɗaya. Yana mai cewa abin da jamaá ke buƙata shine zaman lafiya da kwanciyar hankali da cikakken tsaro suna kuma son ganin alámura sun koma kamar yadda suke.

Kofi Annan yace zai sami ganawa da shugaba Mwai Kibaki da Raila Odinga domin shaida musu cewa jamián da suka naɗa ba zasu iya warware matsalar ba, a saboda haka alamura na hannun su idan ana son sami cigaba to wajibi su da kan su, su shigo ciki. Wata majiya ta kusa, tace Kofi Annan ya yi barazanar janyewa daga shiga tsakani idan ɓangarorin biyu suka cigaba da jan kafa domin kawo jinkiri a shawarwarin dake gudana. A waje guda kuma sakatariyar harkokin wajen Amirka Condoleezza Rice ta soki lamirin shugabannin ƙasar ta Kenya a dangane da rashin bada cikakken haɗin kai don kawo ƙarshen wannan rikici, tana mai cewa Washington na duba yiwuwar ɗaukar matakai akan waɗanda ke yin ƙafar ungulu ga ƙoƙarin da ake na sasantawa. Condoleezza Rice ta ƙara da cewa makomar dangantakar Amirka da kowanne daga cikin ɓangarorin biyu ya dogara ne ga haɗin kan da suka bayar wajen samun nasarar warware badaƙalar siyasar da ƙasar ta shiga.

A halin da ake ciki shugaban ƙasar Tanzania Jakaya Kikwaete kuma shugaban ƙungiyar gamaiyar Afirka ya isa ƙasar Kenyan a ziyarar wuni guda domin nazarin cigaban da aka samu na sasantawar rikicin. Ɓangarorin biyu dai na yan siysar ƙasar ta Kenya dake gaba da juna sun amince da samar da gurbi na mukamin Firaminista amma kuma sun sami rarrabuwar kawuna a game da ƙarfin ikon da ya kamata a baiwa wannan matsayi inda ɓangaren gwamnati ke cewa shugaban ƙasar zai cigaba da riƙe ƙarfin ikon da ya saba. Yayin da a hannu guda kuma jamíyar ODM ta Raila Odinga ke buƙatar raba daidai a sauran muƙaman gwamnati. Jamíyar ta ODM ta ci alwashin kiran magoya bayan ta su gudanar da zanga zangar lumana a ranar Alhamis idan buƙatun ta basu biya ba. A yanzu dai hankula sun ɗan kwanta a ƙasar ta Kenya bayan tarzomar da ta gudana a watan da ya wuce wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 1000.